Za mu kara karfin lantarki zuwa 6,000MW a 2024 —Minista
Gwamnati na shirin bai wa ƙananan ’yan kasuwa lasisin samar da wutar lantarki tunda masu yi yanzu sun gaza
Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu ya ce, Gwamnati ta ɗaura ɗamarar kara karfin wutar lantarki zuwa megawat 6,000 kafin karshen shekara daga kimanin megawat 4,000 da take samarwa a yanzu
Adelabu ya bayyana hakan ne ga Kwamitin Wutar Lantarki na Majalisar Dattawa da suka ziyarce shi a ofishinsa ranar Litinin.
Ministan ya ce gwamnatin ta ƙuɗuri aniyar samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 6,000 ta daga ruwa da kuma hasken rana ga gidaje da kuma masu harkokin kasuwanci.
Ya ce abin takaici ne yadda iya Megawatt 5,800 ne mafi yawan abin da ake iya samarwa a yanzu.
“Kayan aikin suna can a zube ba isasshiyar kulawa ba, injinan suna ta yin tsatsa.
“Idan aka yi abin da ya dace, za mu iya samar da megawatt 6,000 kafin karshen 2024,” inji shi.
Ministan ya kuma ce Gwamnatin Tarayya za ta sauya fasalin Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki (DisCos).
Saboda idan DisCos ba sa aiki yadda ya kamata, to ba za a ga ƙoƙarin da gwamnatin ke yi ba.
“Muna matsawa Hukumar Wutar Lantarki (NERC) lamba kan ta tabbatar da cewa DisCos sun tsaya da kafafunsu, idan kuma ta kama a janye lasisinsu saboda rashin yin aiki yadda ya dace, me zai hana?
“Muna shirin rarraba DisCos, za mu rage musu nauyi saboda wasu daga cikinsu aiki ya yi musu yawa don haka dole a samu rashin inganci a gudanarwarsu.”
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito Ministan na cewa lokaci ya yi da gwamnatin tarayya da na jihohi za su fara amfani da damarsu a harkokin gudanarwar wutar lantarki.
“Mun bari kamfanoni masu zaman kansu sun gudanar da harkokin wuta a ƙasar nan na dogon lokaci, kuma sun lalata harkar.
“Muna shirin ba da dama ga kananan DisCos da ke shirye su shigo cikin harkar don saka hannun jari.”