Za mu kara soke lasisin wasu masu hakar ma’adanai a bana — Alake
Ana fama da matsalar masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a Najeriya.
Gwamnatin Tarayya ta sanar cewa a wannan shekarar ta 2024 za ta karbe lasisin karin wasu kamfanoni masu hakar ma’adanai a kasar.
Ministan Albarkatun Kasa, Dokta Dele Alake ne ya bayyana hakan a sakonsa na sabuwar shekarar 2024 a jiya Litinin a gidansa da ke Jihar Legas.
- Jirgin sama dauke da mutane 378 ya kone a Japan
- Gwamnatin Najeriya ta dakatar da tantance takardun digiri na jami’o’in Benin da Togo
Mista Alake ya kara da cewa gwamnati tana gayyatar masu zuba jari daga kasashen ketare a fannin hakar ma’adanan, don haka zamanin kin biyan gwamnati hakkinta ya wuce.
Ana fama da matsalar masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a kasar, da masu lasisin da ba sa biyan kudaden haraji a fannin hakar ma’adanan.
Idan ba a manta ba, a watan Nuwambar bara ne Gwamnatin Najeriyar ta sanar da soke lasisin kamfanonin hakar ma’adinai 1,633 daga hannun wadanda ba su biya kudaden da ya kamata su biya gwamnati da suka hada da haraji ba.
Sai dai tun kafin gwamnatin ta dauki wannan mataki, wasu daga cikin jihohin kasar daga cikinsu har da Jihar Neja suka dakatar duk wasu harkokin hako ma’adanan.