Za mu kashe malamai da sarakuna da ’yan siyasa – Boko Haram

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya bayyana cewa za su kashe wadansu malaman addinin Musulunci da sarakuna da ’yan siyasar Arewacin kasar nan, saboda goyon bayan mulkin dimokuradiyya da suke yi. Ya yi wannan bayanin ne a cikin wani faifan bidiyo da ya fitar a shekaranjiya Laraba, inda ya ce su suka kashe malamin […]

Za mu kashe malamai da sarakuna da ’yan siyasa – Boko Haram

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya bayyana cewa za su kashe wadansu malaman addinin Musulunci da sarakuna da ’yan siyasar Arewacin kasar nan, saboda goyon bayan mulkin dimokuradiyya da suke yi.
Ya yi wannan bayanin ne a cikin wani faifan bidiyo da ya fitar a shekaranjiya Laraba, inda ya ce su suka kashe malamin addinin Musuluncin nan na Zariya Sheikh Muhamma Awwal Albani, kuma ya yi rantsuwar cewa mayakansa su sha alwashin tarwatsa cibiyoyin hakar mai da ke yankin Neja-Delta.
Shekau ya bayyana alkawarin da kungiyarsa ta dauka na yunkurin kashe muhimman shugabannin Arewa, wadanda suka hada da ’yan siyasa da malaman addini da sarakunan gargajiya, wadanda suka ce sunan goyon bayan dimokuradiyya da akidun Yammacin Turai, wadanda a cewarsa sun saba wa addinin Musulunci.
A cikin kaset din bidiyon da ya shafe mintuna 28 yana jawabi a cikin harshen Hausa, kuma ya fito ne a cikin kayan sojoji, sanye da rawani.
Ya lissafo wadanda suka ce za su kashe da suka hada da “(Sheikh Sani)Yahaya Jijngir Shugaban (Majalisar) Malamai ta (kungiyar Izala ta kasa da ke) Jos, jagoran halatta Boko, ko? Mu ne Boko Haram, kai kuma Boko Halal…. Mun kashe Albanin Zariya. Shekau ya kashe Albanin Zariya. Gobe zai kashe Jingir, jibi ya kashe Dapchia (Limamin Jami’ar Maiduguri), wata rana ya kashe Wapchama (Babban Limamin Maiduguri), wata rana zai kashe Shehun Barno da Ado Bayero. Mun yi muku tawaye, tsakaninmu da ku kiyayya ce da mummunar fata har sai kun yi imani da Allah,” inji shi.
Ya kara da cewa: “Dalilin kisan da zan yi muku shi ne saboda ku kafirai ne, kuna bin dimokuradiyya. Duk wanda ya bi dimokuradiyya ya zama kafiri. Wannan shi ne Shekau, wannan shi ne dalilin gaba ta da ku.”
Ya kuma yi jawabi cikin harshen Larabci a wani bidiyon, amma sakon da ya aike duk daya ne da irin wanda ya yi a cikin harshen Hausa.