Za mu kawar da Buhari a zaben 2019 – Sheriff
Sabon nadadden Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa kuma tshon Gwamnan Jihar Borno Sanata Ali Modu Sheriff, ya ce za su kawar da Shugaban kasa Muhammdu Buhari a zaben shekarar 2019.Sanata Ali Modu Sheriff ya bayyana haka ne a shekaranjiya Laraba, kwana daya da nada shi shugaban riko na Jam’iyyar PDP. Ya ce babu abin da […]
Sabon nadadden Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa kuma tshon Gwamnan Jihar Borno Sanata Ali Modu Sheriff, ya ce za su kawar da Shugaban kasa Muhammdu Buhari a zaben shekarar 2019.
Sanata Ali Modu Sheriff ya bayyana haka ne a shekaranjiya Laraba, kwana daya da nada shi shugaban riko na Jam’iyyar PDP. Ya ce babu abin da zai hana jam’iyyarsa wadda ta fadi a zaben bara kawar da gwamnatin Jam’iyyar APC.
Sanata Ali Sheriff wanda da shi aka kafa Jam’iyyar APC ya koma Jam’iyyar PDP ne a karshen shekarar 2014 a daidai lokacin da ake kokarin fuskantar zaben bara.
Sheriff ya bayyana haka ne a Umu’ahiya fadar Jihar Abia a lokacin bikin addu’o’in nuna godiya da aka shirya don taya Gwamnan Jihar Okezie Ikpeazu murnar samun nasara a Kotun koli, bayan da a ranar 3 ga Fabrairu kotun ta tabbatar da nasararsa a zaben 11 ga Afrilun bara.
Sanata Sheriff, ya ce kwanan nan PDP za ta fito da tsarinta na yadda za ta kayar da APC daga mulki. “Muna nan a yau, inda za mu fara daga nan, kuma za mu shiga fadar Shugaban kasa ta Aso Rock a shekarar 2019 insha Allah,” inji shugaban.
Ya kara da cewa “Daga nan za mu tafi tare. Wannan doguwar hula tawa na shirya in jagoranci abokaina da ’yan uwana zuwa Aso Rock insha Alllah. Kuma da yardarm Allah babu abin da zai hana mu zuwa Aso Rock a shekarar 2019. Kafin lokacin mun tsara shirinmu kuma ina da tabbacin (APC) za su koma inda suka fito, kuma insha Allah babu abin da zai hana mu.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari dai bai ce zai sake tsayawa takara a zaben shekarar 2019 bayan karewar wa’adinsa na farko ba.
Sanata Sheriff ya ce irin mutanen da ya gani a filin wasan da aka gudanar da bikin ya nuna Gwamna Okezie na da goyon bayan jama’ar da suka zabe shi.
“Daga abin da nake gani a filin wasa a fili yake cewa zabensa zabe ne na al’umma. Zabe ne da Allah Ya kaddara…. Zabe ne na jama’a,” inji shi.
Da yake jawabi a madadin gwamnonin PDP, Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose ya ce canji da kasar nan take fata yana iya zama wata ‘dama.’
Gwamnonin PDP da suka halarci bikin su hada da Nyesome Wike (na Ribas) da Ifeanyi Okowa (na Delta) da Udom Emmanuel (na Akwa Ibom) da Mataimakin Gwamnan Ebonyi wanda ya wakilci Gwamna Dabid Umahi. Gwamnonin hudu kamar Okezie Kotun koli ce ta tabbatar da zabensu.