Za mu kawar da ‘yan ta’adda — Shugaban Tunisiya

Shugaban kasar Tunisiya, Beji Ceid Essebsi ya sha alwashin fuskantar kawar da ta’addanci daga kasar bayan harin da aka kai babban birnin kasar, Tunis shekaranjiya Laraba. Shugaba Essebsi, wanda ya yi bayani ga ‘yan kasar ta gidan talabijin cikin kakkausar murya, ya lashi takobin kawo karshen wadanda suka kai hari a kan gidan adana kayan […]

Za mu kawar da ‘yan ta’adda — Shugaban Tunisiya
Za mu kawar da ‘yan ta’adda — Shugaban Tunisiya

Shugaban kasar Tunisiya, Beji Ceid Essebsi ya sha alwashin fuskantar kawar da ta’addanci daga kasar bayan harin da aka kai babban birnin kasar, Tunis shekaranjiya Laraba.

Shugaba Essebsi, wanda ya yi bayani ga ‘yan kasar ta gidan talabijin cikin kakkausar murya, ya lashi takobin kawo karshen wadanda suka kai hari a kan gidan adana kayan tarihi a birnin Tunis.
Ya kara da cewa: “Ina son al’ummar Tunisiya su fahimci cewa muna fuskantar barazanar yaki daga ‘yan ta’adda. Ba za mu yarda wadannan tsirarun mutanen masu kishin jinin mutane su sanya mana firgici ba, za mu sa-kafar-wando-daya da su har sai mun ga bayan su ba tare da tausaya musu ba”.
Harin dai na ci gaba da shan suka daga kasashen duniya da daidaikun mutane.
Kwamitin sulhu na Majalisar dinkin Duniya ya ce aikin ‘yan ta’adda ba zai sauya alkiblar kasar Tunisiya daga turbar dimukradiyya ba.
Babban Sakataren Majalisar, Banki-Moon da shugaban Amurka Barack Obama su ma sun yi Allah-wadai da harin.
Harin dai na shekaranji Laraba ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 19 da suka hada da ‘yan yawon bude ido su 17 da kasashen Japan da Italiya da Columbiya da Spain da Faransa da kuma Australiya da Poland, sai kuma jikkata mutane 40 da ya haddasa.