Za mu kawo canji wajen kyautata rayuwar al’ummar Bassa – Sarah Bali

Shugabar riko ta karamar Hukumar Bassa a Jihar Filato Misis Sarah Bali ta ce za su yi iyakar kokarinsu wajen kawo canji na kyautata rayuwar al’ummar karamar hukumar. Misis Sarah Bali ta bayyana haka ne a lokacin da take rantsar da Sakataren karamar Hukumarda kansilolin riko na karamar hukumar a garin Bassa.Ta ce ganin irin […]

Za mu kawo canji wajen kyautata rayuwar al’ummar Bassa – Sarah Bali
Za mu kawo canji wajen kyautata rayuwar al’ummar Bassa – Sarah Bali

Shugabar riko ta karamar Hukumar Bassa a Jihar Filato Misis Sarah Bali ta ce za su yi iyakar kokarinsu wajen kawo canji na kyautata rayuwar al’ummar karamar hukumar.
Misis Sarah Bali ta bayyana haka ne a lokacin da take rantsar da Sakataren karamar Hukumar
da kansilolin riko na karamar hukumar a garin Bassa.
Ta ce ganin irin yadda aka bar karamar hukuma a baya, a bangarori da dama ya zama wajibi a gare su tashi tsaye su yi amfani da wannan dama da aka ba su, wajen ba da gudunmawarsu don ci gaban karamar hukumar.
Ta ce, “Ya zama dole mu tashi mu yi kokari wajen ganin mun hada kan al’ummar wannan karamar hukuma don a kara samun zaman lafiya da ci gaba.
Misis Sarah Bali ta ce, kofarsu a bude take ga dukkan al’ummar wannan karamar hukuma. Don haka ta yi kira ga al’ummar yankin su ba su goyon baya da hadin ka domin cimma kudirin da suka sanya a gaba, na samar da zaman lafiya da ayyuka yi a karamar hukumar.
Sakataren karamar Hukumar da aka rantsar shi ne Mista Joseph Agun, yayin da aka rantsar da Zaki Bulus da Izaideh Stephen da danjuma Abere da Monday Simon Kadiya da Lukas Ahak Akpai a matsayin kansilolin riko na karamar hukumar.

Gwamnoni ku magance talauci da rashin tsaro —Sarkin Musulmi 

Amarya ta yanke maƙogwaron ango a Kano

NAJERIYA A YAU: Masu nau’in jinin AS sun fi masu AA lafiya — Masana

ADC za ta ƙalubalanci hukuncin soke mata rajista