Za mu kawo karshen hare-haren barayin shanu – Masari

Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya ce, gwamnatinsa za ta yi bakin kokarinta wajen shawo kan matsalar hare-haren da barayin shanu ke kaiwa da ke neman zama baraza ga al’umma.  Gwamna Aminu Masari ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyarar jajantawa ga al’ummar garin Tsakiya a karamar Hukumar Safana a ranar […]

Za mu kawo karshen hare-haren barayin shanu – Masari
Za mu kawo karshen hare-haren barayin shanu – Masari

Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya ce, gwamnatinsa za ta yi bakin kokarinta wajen shawo kan matsalar hare-haren da barayin shanu ke kaiwa da ke neman zama baraza ga al’umma. 

Gwamna Aminu Masari ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyarar jajantawa ga al’ummar garin Tsakiya a karamar Hukumar Safana a ranar Juma’ar da ta gabata kan harin da ake zargin barayin shanu da kai musu a daren Alhamis inda mutum uku suka rasu.
Bayanai sun ce bayan kashe mutanen, maharan sun kone shaguna a cikin garin tare da kora shanun da har zuwa hada wannan rahoto ba a san adadinsu ba.
Gwamna Masari ya nuna alhininsa tare da yin ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu ya ce, gwamnatinsa za ta yi kokarin tabbatar da tsaro a duk fadin jihar, kuma ya bukaci al’ummar jihar su ci gaba da yin addu’ar samun zaman lafiya a jihar da kasa baki daya. Dajin Rugu da karamar Hukumar Safana ke iyaka da shi yah ade da kananan hukumomin Jibiya da Batsari da danmusa da kankara da Sabuwa ya yi iyaka da jihohin Kaduna da Zamfara da Kebbi da Sakkwato baya ga ita Katsina kuma yankin na fuskantar hare-haren barayin shanun a ’yan shekarun nan.
Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina ta tabbatar da faruwar harin da rasuwar mutum biyu, inda ta ce tuni jami’anta suka dukufa wajen bincike domin kamo barayin shanun, kamar yadda suka yi nasarar kama wasu barayin shanun da suka yiwo satar a karamar Hukumar danja suka shiga hannu a karamar Hukumar dandume.