Za mu kera makamin nukiliya matukar Iran ta kera- Saudiya

Yariman Saudiyya mai jiran gado ya yi gargadin cewa kasar Saudiya ma za ta kera makamin nukiliya idan har Iran ta mallaki makamin. Yarima mai jiran gado Mohammad bin Salman ya yi wannan bayanin ne a lokacin da yake zantawa da kafar yada labarai ta CBS, inda ya nuna cewa kasar Saudiya ba ta son […]

Za mu kera makamin nukiliya matukar Iran ta kera- Saudiya

Yariman Saudiyya mai jiran gado ya yi gargadin cewa kasar Saudiya ma za ta kera makamin nukiliya idan har Iran ta mallaki makamin.

Yarima mai jiran gado Mohammad bin Salman ya yi wannan bayanin ne a lokacin da yake zantawa da kafar yada labarai ta CBS, inda ya nuna cewa kasar Saudiya ba ta son makaman nukiliya, amma kuma idan har Iran ta mallaki makamin na nukiliya, “za mu kera namu ba da cikin sauri," a cewarsa.

Hakanan kuma a cikin tattaunawar da aka yi da shi, Yariman ya kira Ayatollah Ali Khamenei a matsayin Hitler.