Za mu kwato biliyoyin kudin da aka sace – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin kwato biliyoyin kudin da jami’an gwamnati suka yi amfani da mukamansu suka sace a baya-bayan nan.Kuma ya sha alawashin dakile duk wata hanya ta sace dukiyar jama’a a lokacin mulkinsa. Shugaban kasa Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da gwamnonin kasar nan a fadar […]

Za mu kwato biliyoyin kudin da aka sace – Buhari
Za mu kwato biliyoyin kudin da aka sace – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin kwato biliyoyin kudin da jami’an gwamnati suka yi amfani da mukamansu suka sace a baya-bayan nan.Kuma ya sha alawashin dakile duk wata hanya ta sace dukiyar jama’a a lokacin mulkinsa.

Shugaban kasa Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da gwamnonin kasar nan a fadar Shugaban kasa da ke Abuja a ranar Talata kamar yadda kakakinsa Femi Adeshina ya ruwaito.
Shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi gwamnonin jihohin kasar nan cewa zamanin yi wa doka karan-tsaye da almundahana da dukiyar al’umma ya wuce.
“Watanni uku masu zuwa za su kasance masu tsauri, amma kuma za mu yi iyakar kokarinmu domin kwato biliyoyin dalolin da aka sace,” Buhari ya shaida wa gwamnonin.
Shugaba Buhari ya ce nan da mako hudu za a fitar da bayani dalla-dalla ga jama’a kan halin da tattalin arziki da dukiyar da gwamnatinsa ta gada suke ciki.
Ya ce “Akwai ka’idojin sarrafa kudi da gudanar da mulki a kowace hukumar gwamnati, amma duk an yi watsi da su a baya.”
Gaskiya matsalolinmu manya ne, amma za mu “There are financial and administratibe Ya nuna mamakinsa kan yadda gwamnoni suka bari aka rika tafka barnar da ake zargi a Asusun Rarar Man fetur tun shekarar 2011, inda ya yi alkawarin magance matsalar.
Buhari ya nanata cewa daga yanzu ba za a rika saka kudaden harajin da Gwamnatin Tarayya take samu a wani asusu ba, baya ga Asusun Tarayya, domin yin haka ya saba wa tsarin mulki.
Ya ce abin da ya ji na gudana a hukumomi da dama musamman kamfanin main a kasa (NNPC) hakika haramtacce ne. Game da mayar wa gwamnatocin jihohi kudaden da suka kashe kan ayyukan tarayya, Buhari ya ba gwamnonin tabbacin cewa Gwamnatin Tarayya za ta biya, amma ya nanata cewa wajibi ne a bi ka’ida.
Ya yi alkawarin bayar da tallafi na musamman ga jihohin Arewa maso Gabas da ta’addancin Boko Haram ya yi wa illa.
Game da tallafa wa jihohin da ake bi bashin albashi Buhari ya ce wani kwamiti da Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo zai shugabanta zai duba Asusun Rarar Man fetur don ganin abin da za a yi a kai cikin gaggawa.
Gwamnonin a karkashin Shugaban Majalisar Gwamnonin Najeriya, Abdul’aziz Yari na Jihar Zamfara, sun mika wa Buhari wasu bukatu da suka hada da bin hukuncin Kotun koli kan dukkan kudaden da ake sanyawa a Asusun Ko-ta-Kwana na Tarayya da mayar musu da kudaden da suka kashe kan ayyukan Gwamnatin Tarayya a jihohinsu da tallafa wa jihohi uku da hare-haren Boko Haram ya illata a Arewa maso Gabas da kuma cikakken bayaninkudaden da aka tara a Asusun Rarar Man fetur tun daga shekarar 2011 da yadda kudaden suka sulale ba tare da an raba su a hukumance ba.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna