Za mu kwato kudin Neja da aka sace – Gwamna
Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello ya nanata kudirin gwamnatinsa na kwato kudin jihar aka yi amfani da dabaru daban-daban domin sace su inda mutane kalilan suka amfana, sannan hakan ya jefa miliyoyin al’ummar jihar musamman mazauna karkara cikin mawuyacin hali.Gwamna Abubakar Sani Bello ya bayyana haka ne yayin mika wa Majalisar Dokokin Jihar […]
Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello ya nanata kudirin gwamnatinsa na kwato kudin jihar aka yi amfani da dabaru daban-daban domin sace su inda mutane kalilan suka amfana, sannan hakan ya jefa miliyoyin al’ummar jihar musamman mazauna karkara cikin mawuyacin hali.
Gwamna Abubakar Sani Bello ya bayyana haka ne yayin mika wa Majalisar Dokokin Jihar kudirin kasafin kudin bana da ya kai Naira biliyan 74 da miliyan 100, inda ya nuna kwarin gwiwarsa kan amfani da tsarin ajiya a asusu bai-daya.
Ya ce, wannan tsari zai taimaka wa gwamnati wurin gano irin badakalar da aka yi ta tafkawa na karkata dukiyar jama’a.
Gwamnan ya ce, “gwamnati mai ci ba za ta amince da cin hanci da rashawa ba.Wannan ya sa ya zama wajibi mu kwato wa jama’armu makudan kudin da aka sauya musu akala ta hanyoyi da dama. Bayan an amso kudin kuma za a gurfanar da duk wadanda ke da hannu a cikin badakalar a gaban kotu domin hukunta su daidai da laifin da suka aikata.”
Ya ce, gwamnatinsa ba ta samu sisin kwabo a baitulmalin jihar ba, don haka suka kwantar da hankulansu har Allah Ya taimaka musu suke gudanar wa jama’a muhimman ayyukan da ke da tasiri a rayuwarsu.
Gwamna Abubakar Bello ya ce kasar nan ta samu kanta a tsaka-mai-wuya sakamakon faduwar farashin man fetur a duniya, ya ce hakan ya sa dole gwamnatinsa ta sake tunanin hanyoyin bi domin kara samun kudin shiga ta yadda za ta samu damar cika alkawuran da ta yi wa jama’ar da suka zabe ta.
Ya jinjina wa ’yan majalisar kan hadin kan da suke ba shi tare da gabatar da kudirori masu tasiri da za su taimaka wurin cimma manufofin jam’iyyarsu ta APC.
Shugaban Majalisar Alhaji Ahmad Marafa Guni ya tabbatar wa Gwamnan hadin kansu wurin nazarin kasafin da amincewa da shi domin dora jihar a turbar ci gaba.
Alhaji Marafa Guni ya ce majalisar za ta yi rangadin gani-da-ido don ganin ayyukan da ma’aikatu da hukumomin gwamnati suka yi alkawarin aiwatar wa jama’a a kasafin na bana, inda ya ce lokaci ya wuce da za a yaudari talakawa ta hanyar yi musu dadin baki.