Za mu la’anci masu la’antar gwamnatin Buhari – Sheikh Alhassan Sa’eed

Wani fitattacen malamin addinin Musulunci da ke Jos a Jihar Filato kuma jigo a kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Alhassan Sa’eed Adam Jos ya ce talakawan Najeriya za su la’anci duk wadanda suka la’anci gwamnati Shugaban kasa Muhammad Buhari kan halin da ake ciki a kasar nan. Sheikh Alhassan Sa’eed […]

Za mu la’anci masu la’antar gwamnatin Buhari – Sheikh Alhassan Sa’eed
Za mu la’anci masu la’antar gwamnatin Buhari – Sheikh Alhassan Sa’eed

Sheikh Alhassan Sa’eed Adam Jos Wani fitattacen malamin addinin Musulunci da ke Jos a Jihar Filato kuma jigo a kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Alhassan Sa’eed Adam Jos ya ce talakawan Najeriya za su la’anci duk wadanda suka la’anci gwamnati Shugaban kasa Muhammad Buhari kan halin da ake ciki a kasar nan.
Sheikh Alhassan Sa’eed Jos ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen rufe taron kara wa juna sani na kwana uku kan zaman lafiya da hadin kai da kungiyar Izala reshen karamar Hukumar Jos ta Arewa ta shirya.
Ya ce masu sukar gwamnatin Buhari ’yan adawa ne da masu hassada da malaman tsibbu da azzaluman ma’aikata da barayin gwamnati da suka sace dukiyar jama’ar kasar nan. Ya ce irin wadannan mutane ne suke sukar wannan gwamnati suke la’antarta, suna cewa wai ana cikin wani mawuyacin hali a kasar nan.
Sheikh Alhassan Sa’eed ya ce a gwamnatin da ta gabata dukkanmu idan muka fito daga gidajenmu muna ganin kamar ba za mu iya komawa gidajenmu ba, saboda halin da ake ciki. Amma yanzu wannan tsoro ya kau sakamakon zuwan wannan gwamnati. “A baya noma da kiwon da muke yi a Arewa ’yan Boko Haram sun hana. Duk inda mutum zai je a fargice yake, duk ba mu ga wannan bala’i da Allah Ya kawar mana ba, shi ne ake cewa kasa ta shiga matsi? Shin matsin da muka shiga na kisa da ake yi mana a lokacin gwamnatin da ta gabata, amma yanzu an zo an dakile wadannan miyagun abubuwa shi ne ake cewa an shiga matsatsi? Saboda haka muna kira ga talakawan Najeriya, su gane cewa masu wadannan soke-soke suna yi ne don bata wannan gwamnati. Kuma muna kira ga ’yan Najeriya mu ci gaba da yi wa wannan gwamnati addu’o’in alheri mu yi yi watsi da masu wadannan soke-soke,” inji shi.
Bababn bako mai jawabi kuma Babban Sakataren kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta kasa Sheikh Khalid Aliyu Abubakar ya ce addinin Musulunci ba addini ne na tashin hankali ba, ba
addini ne na ta’addanci ba, addini ne na zaman lafiya da cigaba. Don haka ya yaba wa kungiyar Izala kan wannan taro na zaman lafiya da ta shirya.
Sheikh Khalid Aliyu wanda Sakataren Majalisar Musulmin Jihar Filato (Council of Ulama), Barista Auwal Abdullahi ya wakilta ya ce idan aka dubi ayyukan kungiyar Izala za a fahimci cewa kungiya ce da take kokarin ganin an samu zaman lafiya a tsakanin al’ummar Najeriya.
Don haka ya yi kira ga sauran kungiyoyi kan su rika shirya irin wadannan tarurruka na wayar da kan al’umma kan muhimmancin zaman lafiya.
Tun da farko a jawabin shugaban kungiyar Izala na karamar hukumar Alhaji Ya’u Musa Maigado ya ce babban burinsu na shirya wannan taro, shi ne su ga cewa zaman lafiya da zamantakewa sun kara habaka a garin Jos da kasa baki daya. Ya ce don haka ne ma suka
gayyaci wadanda ba Musulmi ba zuwa wajen taro domin dada nuna wa duniya cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali ya samu a Jihar Filato.