Za mu magance matsalar farashin kayan abinci — FCCPC
Gwamnati ta damu matuƙa game da yadda talakawa ke fama da tsadar kayan abinci.
Hukumar Kare Hakkokin Masu Amfani da Kayayyaki ta Kasa (FCCPC) ta ce, Gwamnatin Tarayya za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin farashin kayayyakin abinci ya karye a kasar nan.
Shugaban Hukumar FCCPC ta Kasa, Dokta Adamu Abdullahi ne ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar Kasuwar Hatsi ta Dawanau a Jihar Kano.
Dokta Abdullahi ya ce, ya je kasuwar ce don su gano abin da ke faruwa da ya janyo tsadar kayan abinci tare da ba wa gwamnati shawarwari don daukar matakin da ya dace.
“Gwamnati ta damu matuƙa game da yadda talakawa ke fama da tsadar kayan abinci.
“Don haka muka zo mu ga abin da ke faruwa tare da tattaunawa da ’yan kasuwar don sanin matsalolinsu da samun shawarwarinsu domin magance abin da ke faruwa don sama wa mutane sauki.
Ya ce, bincikensu ya gano cewa, babu wani abu na daban da ya janyo hakan sai yanayin kasuwa.
Ya yi alkawarin mika shawarwarin ’yan kasuwar ga gwamnati don samun mafita ta yadda kayan abinci za su sauka don talakawa su rika samu cikin sauki.
“Babbar shawarar da Gwamnatin Tarayya za ta fara amfani da ita, ita ce ta shigo da kayan abinci cikin kasar nan wanda ake tunanin idan abincin ya yawaita farashin zai karye,” in ji shi.
Shugaban ’Yan Shinkafa ta Kasuwar Dawanau, Alhaji Abdulkadir Umar ya ce, suna samun shinkafar ce da tsada tun daga wajen sayo ta a kasuwannin kauyuka.
Ya dora alhakin tsadar shinkafar ga karancin abinci da aka samu sakamakon rashin yin noma.
“Akwai karancin yin noman ba kamar a baya ba, wanda ake ganin hakan ya faru ne saboda rashin tsaro da ke addabar wasu sassa na kasar nan,” in ji shi.
Ya ce, “Zai yi kyau Gwamnati ta shigo ciki ta inganta harkar noma ta hanyar sanar wa manoma taki a kan farashi mai sauki.
“Haka kuma, akwai bukatar a inganta tsaro yadda manoma nan za su ji dadin yin shuka da girbi cikin aminci ba tare da tsoro ko fargaba ba.
“Hakan zai sa a samu wadataccen abinci a kasa.”
Shugaban ’Yan Masara na Kasuwar, Alhaji Jamilu Abdullahi ya dora alhakin tsadar kayan abinci a kan yanayin rani da ake ciki.
“Dama an saba samun haka a duk lokacin rani, saboda an kusa cinye tsoho ga saboda bai zo ba. To sai ki ga farashin ya tashi. Duk da cewa na wannan shekarar ya fi tsanani,” in ji shi.
’Yan kasuwar sun shawarci Gwamnatin Tarayya da ta dawo da tsarin sayen kayan abinci daga manoma a farashi mai kyau, inda hakan zai sa manoma su mayar da hankali wajen noma kayan abinci.
Ya ce, “Abin da ke faruwa shi ne manoman da suke noma abinci duk sun daina, sun koma noman kayayyakin sayarwa kamar su ridi da zobo da waken soya da sauransu.
“A duk yayin da manoma suka noma abinci da yawa to farashinsa karyewa yake yi, wanda za ka ga ya kai manomi ga yin asarar maimakon samun riba.
“Hakan ya sa manoman suka janye daga noman kayan abinci, suka koma na kayan sayarwa da ake fita da su kasashen waje.
“Ka yi noma kana tunanin za ka sayar da amfaninka a kan Naira 10, saboda yawan kayan sai farashin ya koma Naira 7.
“Don haka a gaba manomi ba zai saki jiki, ya noma wannan da yawa ba.
“A nan muna kira ga gwamnati idan an samu kayan abinci ya yi yawa a kasa ta rika sayewa daga hannun manoma a farashi mai kyau.”
“Wannan zai sa manoma su ci gaba da yin noma ba tare da fargaba ko tsoron faduwa ba,” in ji shi.
Shi kuwa Malam Abdullahi Ka-sayar-Ka-Bar-su da ke sayar da doya a Kasuwar Dawanau ya danganta tsadar doyar a kan tashin man dizil wajen sufurin doyar daga wasu garuruwa zuwa Kano “Doyar nan dai muna samun ta a Zariya da Neja da Yelwan Shandam da Jalingo.
Idan kuka dubi yadda farashin man dizil da fetur suka yi tashin gwaron zabo, hakan ya shafi farashin doyar.
“Doyar da a da muke sayar da ita Naira 500 yanzu ta koma Naira 4,000, wacce ake sayarwa Naira 1,000 ta zama Naira 6,000,” in ji shi.
Wata mai sayen doya, Madam Justina Ogedo ta ce, “Yanzu na tambayi farashin doyar kanana biyu an gaya min Naira 8,000.
“Ba zan iya saye ba saboda ta yi min tsada. Sai dai in hakura, in nemi wani abin in saya. Muna son mu ci doya, amma ta fi karfin aljihunmu.”