Za mu mayar da martani na ‘jarunta’ kan kisan Soleimani – Janar Ka’ani

Sabon Kwamandan Sojin Juyin Juya-Hali na Iran (IRGC), Janar Esmail Ka’ani ya ce Amurka ta hallaka wanda ya gada, Kassem Soleimani, ‘a yanayi irin na nuna tsoro’ inda ya yi alakawarin ‘kai wa abokiyar gabarsu hari na nuna jarunta’. Esmail Kaani, ya fadi haka ne a farkon makon nan, yayin bikin kaddamar da shi da […]

Za mu mayar da martani na ‘jarunta’ kan kisan Soleimani – Janar Ka’ani

Sabon Kwamandan Sojin Juyin Juya-Hali na Iran (IRGC), Janar Esmail Ka’ani ya ce Amurka ta hallaka wanda ya gada, Kassem Soleimani, ‘a yanayi irin na nuna tsoro’ inda ya yi alakawarin ‘kai wa abokiyar gabarsu hari na nuna jarunta’.

Esmail Kaani, ya fadi haka ne a farkon makon nan, yayin bikin kaddamar da shi da manyan kwamandojin IRGC suka shirya masa domin kama aikin jagorantar rundunar.

“Sun (Amurka) kashe shi (Soleimani) a yanayi irin na nuna tsoro da rashin jarunta, amma cikin yardar Allah da karamcinSa ga masu neman ’yanci a fadin duniyar nan, za mu hari makiyansa cikin yanayi na gwada jarunta,” inji shi.

Kisan Soleimani a wani hari da Amurka ta kai a ranar 3 ga Janairu a filin jirgin sama na Bagadaza ya haifar da fargabar yiwuwar barkewar yaki tsakanin Amurka da Iran, sai dai fargabar ta kau bayan wasu hare-haren ramuwar gayya da Iran ta kai ranar 8 ga Janairu kan wasu sansaonin Amurkar a Iraki da ba su kashe ko dan tsako ba.

Jagoran addini na kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei,  ya yi kiran da janye korar Amurka dungurumgum daga Gabas ta Tsakiya.

Rundunar IRGC

Mayakan da ake kira da dakarun Kuds na daga cikin sojoji dubu 125 na Rundunar IRGC, wani rukunin mayakan da ba soji ba da ke karbar umarni kai-tsaye daga jagoran addini na kasar shi kadai.

Rundunar IRGC ita ce ke kula da harkokin makamai masu linzami na Iran; kuma tana da reshen mayakan ruwa kusa da sansanin sojin ruwan Amurka a yankin Tekun Pasha – kuma tana da hadaka da dakarun  sa-kai na Basij.

A karkashin Soleimani, Rundunar Kuds ta taimaka wajen yada karfin da Iran ke da shi a yankin Gabas ta Tsakiya – ta hanyar kafa rassa a kasashen yankin.

A kasar Syria, rundunar ta taka rawa wajen mara baya ga Shugaban Kasar Bashar al-Assad bayan da kasar ta fada cikin yaki.

Ta kuma horar tare da bayar da makamai ga kungiyoyin mayakan sa-kai da suka taimaka wajen murkushe Kungiyar ISIL/ISIS a kasashen Syria da Iraki.

Ayatollah Khamenei, yayin sanar da nadin Janar Kaani ranar 3 ga Janairu, ya ce sabon Kwamandan Dakarun Kuds guda ne cikin ‘jiga-jigan kwamandojin rundunar IRGC’ a shekarun 1980-1988 lokacin da Iran ta gwabza da makwabciyarta Iraki; inda ya bayyana a karkashin sabon kwamandan, rundunar za ta ci gaba da bin tafarkin tsohon kwamandanta Janar Soleimani.

Ko a lokacin jana’izar tsohon kwamandan, Janar Kaani, mai shekara 62, ya yi alwashin ci gaba da bin tafarkin wanda ya gada wajen jagorantar rundunar, inda ya ce: “Za a mayar da martanin kisan Soleimani ta hanyoyi da dama ta hanyar kawar da Amurka daga yankin.”

 

Jagoranci da rayuwar Janar Kaani

An haife shi a karshen shekarun 1950 a birnin Mashhad da ke Arewa maso Gabashin Iran, Kaani ya shiga rundunar IRGC a 1980, watanni kadan kafin kutsen da sojojin Iraki suka yi wa yammacin Iran, wanda ya yi sanadin kazamin yakin da aka shafe shekara takwas ana gwabazawa tsakanin kasashen biyu-da ya yi sanadin salwantar rayuka wajen miliyan guda.

Bayan fara yakin, an rantsar da Kaani a matsayin Mataimakin Babban Hafsan Mayakn Kasa na Rundunar IRGC.

Sai dai babu bayani kan aihinin lokacin da Janar Kaani ya shiga Rundunar Kuds, amma Kamfanin Dillancin Labarai na Iran (IRNA), ya ruwaito cewa an nada shi Mataimakin Kwamandan Mayakan Kasa ne a 1997, a daidai shekarar da aka ayyana Janar Soleimani a matsayin babban kwamandanta.

Ta fuskar tsarin aiki tare da tabbatar da shiga yankuna daban-daban, Soleimani da Kaani sun yi aiki tare wajen taka muhimmiyar rawa domin fadada ikon Iran a kasashe makwabta.

Kadan daga bayanan da ya yi a bainar jama’a, Kaani ya kasance mai sukar Amurka da Isra’ila. A wata makala a shekarar 2017 ya bayyana cewa “Barazanar da Shugaban Amurka Donald Trump ke yi kan Iran za su yi wa Amurkar illar gaske.”

A shekarar 2012, Amurka ta kakaba masa takunkumi inda ta bayyana dalilin matakin kan yadda ta ce yake “tura kudade ga ’yan barandan dakarun Kuds a Nahiyar Afirka da kuma sauran kungiyoyin ’yan ta’adda.”