Za mu mayar da tsofaffin ledoji dukiya – Ministan muhalli
Aminiya ta samu zantawa da karamin Ministan muhalli na Najeriya Alhaji Ibrahim Jibrin, Wamban Nasarawa, a lokacin da ya halarci taron kasa da kasa game da filaye da muhalli da aka yi a Washington na kasar Amurka, inda ya yi bayani game da kokarin da gwamnatin Buhari take yi domin inganta muhalli. Ga yadda hirar […]

Aminiya ta samu zantawa da karamin Ministan muhalli na Najeriya Alhaji Ibrahim Jibrin, Wamban Nasarawa, a lokacin da ya halarci taron kasa da kasa game da filaye da muhalli da aka yi a Washington na kasar Amurka, inda ya yi bayani game da kokarin da gwamnatin Buhari take yi domin inganta muhalli. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya:Da farko za mu so mu ji me ka zo yi a Amurka, musamman Washington?
Minista: Bisimillahi Rahamani Rahim, Abin da ya kawo mu nan Washington taro ne da bankin duniya ya saba shiryawa duk shekara, wannan kuma da muka zo shi ne na 17, kuma taron ya ta’allaka ne a kan filaye da kuma abin da ya shafi muhallin jama’a (LAND AND PROPERTY CONFERENCE), shi ne muka zo wannan taron domin mu duba matsalolin da ke addabar mutane duniya baki daya, kuma wannan taron ya tara kwararru daga jami’o’i da masana daga sassa daban-daban na duniya da manyan ma’aikatun gwamnati da kamfanoni da manyan manoma, domin su tattauna harkokin da suka shafi filaye ko kuma muhalli a duniya baki daya.
Aminiya:Taron ya tattauna matsalolin ne ko har da hanyoyi warware matsalolin?
Minista: Babban bankin duniya yana da sashe na musamman da ya shafi harkar filayen nan, kuma ya kan ba da agaji ko tallafi domin mutane su yi bincike a kasashen duniya, musamman kasashe masu tasowa wadanda suke da matsalolin tattalin arziki. Matsalar filaye a ko’ina a duniya za ka tarar matsala ce ta harkar gona. Akwai wuraren da manyan manoma ko kuma hamshakan masu kudi sukan kanfaci filaye masu dinbin yawa, wannan yakan sa talakawan da suke wadannan wuraren su tashi da sunan manoma, amma ba su da filayen da za su yi noman, gonakin duk gaba daya an handame su. Irin wadannan matsalolin suna kara sanya fatara ko talauci ga mutanen da rayuwarsu ta dogare ne ga aikin noma. Fiye da shekaru 17 din nan bankin duniya yakan sa ana yin bincike, don haka kowace shekara akan zo a taru domin a yi taron kara wa juna ilmi, wadannan matsalolin da aka samu daga kasashe masu tasowa da wadanda suka ci gaba su ne jama’a suke zama su tattauna, kowa ya kawo nasa bayanin, sai a duba a ga yaya ka gyara taka matsalar, shin yadda ka bi ka gyara naka ana iya amfani da irin wannan tsarin domin gyarar matsala a Najeriya ko Ghana? Irin wadannan matsalolin su ne masana suke tattaunawa.
Aminiya; Kwanaki kwararru sun yi magana a kan yawan sare daji a yi noma a kasashe irin su Latin Amurka, irin su Brazil, suka ce yawan sare itatuwa yana yi wa muhalli mummunar illa, shin akwai irin wannan matsalar a Najeriya?
Minista: kwarai muna samun ire-iren wadannan matsalolin, sai dai idan ka dubi girman Brazil da kuma irin dazuzzukan da take da su, na Najeriya bai kai na Brazil girma ba. Amma kuma ba wai yana nufin ba a samun wadannan matsalolin a Najeriya ba ne.Matsalolin da ake samu a wajen kare muhalli da dazuzzuka su ne yawan sare itatuwan nan. Musali, kafin in zo nan Amurka na bar wata matsala a gida wanda ta shafi jihar Kurosribas, akwai wata hanya da ta kai tsawon kilomita 260 jama’a sun taso suna kukan cewa hanyar za ta ratsa wani daji cikin dazuzzukan da gwamnatin tarayya ke kulawa da su kuma dajin nan ya yi suna sosai saboda iri dabbobin da ke cikinsa, musamman irin su gwaggon biri, ka san turawa suna zuwa yawan bude ido kuma suna ganin wadannan dabbobi masu muhimmanci, to ana ganin idan aka yi titi a wannan wurin zai kawo illa ga wannan dajin da ma kurmin da ke wannan wurin. To irin wadannan matsalolin muna samunsu.Kuma ina ganin ministata za ta je ta samu gwamnan su tattauna kan wannan batu domin a san yadda za a kare wannan dajin. Irin wadannan matsalolin suna tayar muna da hankali kwarai da gaske, domin mun san wadannan dazuzzuka suna da muhimmaci saboda suna rage yawan dumamar yanayi. idan aka sare guda ba a shuka wani, kuma ba kudancin Najeriya ba har da arewaci inda babu itatuwan da yawa.Ba shakka akwai matsala babba. Wannan ya sa aka kafa wata hukuma yanzu a karkashin ma’aikatar raya muhalli ta Najeriya, wannan hukumar za ta kula ne da wadansu jihohin Arewa guda 11.
Aminiya:Sabuwa ce hukumar?
Minista:Sabuwa ce, ba ta fi shekaru uku da aka kafa ta ba.Da turanci a ce mata National Agency for the Great Green World, hukuma ce wadda aikin da za a ba ta ya samo asali daga hukumar tarayyar Afirka, wadda ita ce ta kafa wannan hukumar, kuma ta ratsa kasashen Afirka 11, daga yammacin Afirka zuwa gabashinta.
Aminiya:Kana nufin hukumar ce za ta kula da dasa itatuwan da za su zama kamar lema a wannan yankin?
Minista: kwarai da gaske, mu a Najeriya ta ratsa jihohi 11 ne, da suka kunshi kananan hukumomi 44, kuma idan ka duba tsawon itatuwan da za a shuka zai kai kilomita 1,500, tun daga Sakkwato har zuwa Maiduguri, kuma fadinsa zai kai kilomita 15. Wannan babban aiki ne da ake son a yi don a kare yammacin Arewa da kuma Najeriya baki daya daga hadarin gurgusowar hamada.Bincikeya tabbatar cewa rairayin hamada yana kara shigowa na tsawomn mita 400 a kowace shekara, kuma illar da yake yi shi ne, yana rufe kauyuka da wuraren shan ruwan dabbobi, wannan ya sa ake son a shiga dashen itatuwan nan domin su tallafa wajen kare muhalli.
Aminiya: Ko akwai wani abu da gwamnati ke yi da zai samar wa mutane da zabi domin su rage sare itatuwa domin yin makamashi?
Minista: Ba shakka akwai abin da ake yi, gaskiya ne wannan sare itace ya wuce yadda duk mutum yake zato, amma kuma babu yadda za a yi ka hana mutane sare itatuwan nan, domin da shi ne suke makamashi, misali masu gasa biredi, kafin su gasa biredi sai sun sare itatuwa masu dimbin yawa, shi za su sa a wajen gasa biredin, wannan barna ce babba. To me za a yi? Abin da za a yi shi ne, dole a dasa itatuwan fiye da yadda ake sarewa, na biyu dole ka samar wa mutane yadda za su yi amfani da wani zabin amfani da itatuwan ta hanyar kimiyya, misali, idan mutun zai yi amfani da itace biyu ko uku ya zamo daya ma ya wadatar, ko kuma ka samo musu wata hanya da zai hana amfani da wannan itacen. A Najeriya muna da albakar mai da kuma iskar gas, kuma abin da ke faruwa a Najeriya fiye da shekaru aru-aru duk iskar gas din nan kona ta ake yi, idan ka je duk matatun manmu na Najeriya za ka tarar ana kona wannan iskar gas ne.Abin da gwamnati take son yi shi ne, tunda ga harkar mai a duniya ya fara ja baya, farashinsa ya fadi warwas, kuma mun dogara ne a kan mai, abin da shugaba Buhari yake son ya yi kuma ya fara, shi ne a nemi hanyar da Najeriya za ta daina jingina kacokan a kan mai. Kuma shi wannan iskar gas akwai hanyar da ake son a bi, shi ne za a samo hanyar da za a sarrafa wannan iskar gas din ta yadda za a riba shi ta kananan tulu ko bututu ko kuma kuttu, yadda za a rika amfani da shi wajen girki, domin ka san ba abu ne mai sauki ba, musamman ga mutanen da ke karkara, dole sai an gwada musu yadda za su yi amfani da shi.
Aminiya:Wata matsala it ace ta kudin wannan gas na cikin tulu, domin mutumin kauye ba zai iya cire Naira dubu daya ko biyu domin ya sayi gas ba.
Minista: Za a rika sawa a cikin ‘yan kananan tulunan da za a yi, da kuma wadansu murhu da za su rika amfani da gawayi ko kuma dussan katako, kodayake duk wadannan su ma idan ka duba sai ka ga cewa sun ta’allaka ne a kan itatuwa.Don haka dole shirin shuka itatuwa nan ya kankama sosai, domin shi ne kawai mafi sauki, idan an shuka itace a san wanne ne za a yi amfani da shi na makashi, wanne ne za a yi amfani da shi na abinci. Za a shuka su mangwaro da lemu, duk za su tallafa.
Aminiya: Ina son ka yi muna bayani a kan abin da ya shafi leda wacce duk inda ka shiga a Najeriya za ka ganta, musamman na ruwan da ake kira PURE WATER, domin wannan ledar sai ta kwashe kusan shekara 100 ba ta narke ba.
Minista:Wannan tambaye ce mai muhimmaci, ranar juma’a kafin in zo nan Amurka, ni da ministata mun yi tattaki zuwa Kano, daya daga cikin abin da muka yi a can shi ne, mun duba wata masana’anta ce da aka kafa ta sarrafa wadannan ledoji, ledojin nan kamar yadda ka fada, suna da mummunar illa, domin suna dadewa cikin kasa ba su rube ba, kuma mutane sun dogara da shan wannan rowan, kuma kowa ya sha ruwan yar da ledar zai yi, kuma bayan rashin narkewar da ba sa yi, haka kuma sukan toshe magudanan ruwa, abin da hakan kan haddasa ambaliya. Akwai wannan masana’anta a Kano, amma tunda aka kafa ta ba a yi wani abu game da ita ba, shi ya sa muka je muka duba, kuma idan Allah Ya yarda za mu zauna mu rubuta kyakkyawan rahoton yadda za a hada kai da gwamnatin jihar Kano da wadansu kananan hukumomi domin a ga cewa an bude wannan masana’antar, yadda za a rika tara ledojin nan a sake sarrafa su domin sayar wa masu bukatarsu. Wannan ba guda daya ne ba, kusan duk Najeriya ana bukatar wadannan abubuwa. Kamar nan kasashen da suka ci gaba sun dade suna wannan al’amari na sarrafa wadannan ledojin.
Aminiya:Akwai wata doka da gwamnatin tarayya ke tunanin yi ga masu zubar da wadannan ledojin ta yadda zai sa mutane su shiga taitayinsu wajen zubar da ita barkatai?
Minista: Akwai, amma a tsarin irin ta Najeriya akwai gwamnatin jiha kuma akwai na tarayya, domin dokokin da za a yi na shara da kare muhalli irin wadannan gwamnatocin jihohi su ke da hakki na yin ire-iren wadannan dokokin, domin su suka san yadda za ta dace da al’ummarsu, mu abin da muke yi a tarayya shi ne kokarin hada kai ne da jihohi mu tabbatar cewa mun tallafa wa juna domin su kai ga biyan bukata, shi ya sa ma aka kai ga kafa wadannan masana’antu da niyyar idan an gama za a mika wa gwamnatocin jihohi.