Za mu mayar wa ’yan kasuwa kayan abincinsu da muka kwace —Kwastam

Kwastam za ta mayar wa ’yan kasuwa da ta kwace kayan abincin da suka shigo da shi, bisa sharadin ’yan kasuwar ba za su boye kayan abincin ba.

Za mu mayar wa ’yan kasuwa kayan abincinsu da muka kwace —Kwastam

Shugaban Kwastam na Kasa, Bashir Adewale Adeniyi, ya ce hukumar za ta mayar wa ’yan kasuwan da ta kwace abincin da suka shigo da shi kayan nasu.

Adeniyi ya ce Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya ba da umarnin domin ba wa ’yan kasuwa damar shigar da kayan nasu da kuma sayarwa a kasuwanni.

Sai dai ya ce sharadin mayar wa ’yan kasuwan kayan abincin shi ne za su sayar wa ’yan Najeriya ba boyewa za su yi ba.

Adeniyi ya sanar da haka ne a taron masu ruwa da tsaki a yankin Kwangwalam da ke kan iyakar Najeriya da Nijar, a Karamar Hukumar Maiadua ta Jihar Katsina ranar Asabar.

A cewarsa, shugaban kasa ya yi haka ne a kokarinsa na ganin ’yan Najeriya sun samu isasshen abincin saya, wanda a cewarsa zai kawo saukin farashi a kasuwanni.

“A halin yanzu a hannunmu akwai kayan abinci cikin manyan motoci sama da 120 da muka kwace.

“Muna fata idan aka sake su suka shiga kasuwanni a samu sauki.

“Makasudin hakan shi ne samar da tsaro da wadatuwar abinci ga al’ummar Najeriya musamman a wannan hali da ake ciki,” in ji shugaban kwastam din.

A ranar Asabar din shugaban kwastam din ya ziyarci tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura, da kuma fadar Sarkin Daura, Dr Umar Farouq Umar, inda aka ba shi sarautar Mabudin Hausa.

’Yan Bindiga: An miƙa wa gwamnatin Kaduna mutum 58 da aka ceto

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna

Barikin Ladi: Asalin garin da yanayin rayuwar mazauna