‘Za mu maye gurbin ShopRite a Najeriya’

‘Yan kasuwa na gida sun ce a shirye suke su maye gurbin katafaren kantin zamani na kasar Afirka ta Kudu, ShopRite, da ke shirin sayar da hannayen jarinsa da nufin janyewa daga Najeriya. A ranar Litinin ne ShopRite mai rassa a sassan Najeriya ya bayyana aniyarsa ta janyewa daga kasar bayan shafe sama da shekara […]

‘Za mu maye gurbin ShopRite a Najeriya’

Alhaji Sabitu Muhammad Yahaya, Manajan Darektan rukunin kantunan Jifatu

‘Yan kasuwa na gida sun ce a shirye suke su maye gurbin katafaren kantin zamani na kasar Afirka ta Kudu, ShopRite, da ke shirin sayar da hannayen jarinsa da nufin janyewa daga Najeriya.

A ranar Litinin ne ShopRite mai rassa a sassan Najeriya ya bayyana aniyarsa ta janyewa daga kasar bayan shafe sama da shekara 15, saboda abun da ya alakanta da rashin ciniki.

Manajan Darektan rukunin kantunan Jifatu, Alhaji Sabitu Muhammad Yahaya ya ce ko da ShopRite ya bar kasar, to kamfaninsa da makamantansa na cikin gida na da karfin maye gurbinsa.

A jawabinsa ga ‘yan jarida a Kano ya ce, “Gwamnati a Najeriya ba ta karfafa gwiwar kamfanonin gida ta hanyar hulda da su, sun fi gane su yi mu’amala da na kasashen ketare.

“Ba ma samun tallafin da ya kamata daga gwamnati. Idan alal misali bayan duk wannan goyon bayan da kamfanonin kasashen waje ke samu, ShopRite zai yi tunanin barin kasar saboda rashin ciniki, me kake tunani game da ‘yan kasuwar cikin gida kuma?”, inji shi.

Alhaji Sabitu ya kara da cewa gudunmawar da kamfanonin cikin gida ke bayarwa wajen samar da aikin yi da kuma kara wa kasa kudaden shiga ta hanyar biyan haraji ba zai misaltu ba.

Ya ce, “Kamfaninmu alal misali yana da sassa sama da 13 da kuma rassa a jihohi da dama a Najeriya, akwai kuma dubban mutane da ke cin abinci a karkashinmu.

Dan kasuwar ya koka cewa gwamnatoci a matakai daban-daban a kasa na yin watsi da harkokin ‘yan kasa tare da karkata ga ‘yan kasashen waje wadanda ke ketarewa bayan sun samu kudi a Najeriya.

Don haka ya shawarce su da su rika tallafa wa kamfanoni cikin gida ta hanyar sayen hajojinsu ko suma sa samu su yi gogayya da na kasashen wajen.

“Da gwamnatoci za su rika sayayya a wajenmu kamar yadda suke yi a kantunan kasashen waje, da za su sha mamakin yawan mutanen da za mu samar wa da ayyukan yi.

“Nan ba da jimawa ba za mu je jihohi da dama mu bude rassa, har a Afirka ta Kudun sai mun bude da yardar Allah”, inji manajan darektan.