…Za mu murkushe cin hanci kamar yadda muka yi wa Boko Haram – Gwamnati
Gwamnatin Tarayya ta ce za ta murkushe cin hanci da rashawa kamar yadda ta murkushe hare-haren Boko Haram, inda ta ce cin hanci da rashawa ya fara mayar da martani ta hanyar sukar tsare-tsarenta tare da zargin Shugaba Muhammadu Buhari da ‘mai mulkin kama-karya.’Minsitan Watsa Labarai Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana haka a ranar […]
Gwamnatin Tarayya ta ce za ta murkushe cin hanci da rashawa kamar yadda ta murkushe hare-haren Boko Haram, inda ta ce cin hanci da rashawa ya fara mayar da martani ta hanyar sukar tsare-tsarenta tare da zargin Shugaba Muhammadu Buhari da ‘mai mulkin kama-karya.’
Minsitan Watsa Labarai Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana haka a ranar Talatar da ta gabata lokacin da yake ganawa da editocin shiyya na jaridun kasar nan a Abuja.
Minista Lai ya ce babu wanda ya kawar da hankalin Gwamnatin Tarayya ko ya sa ta daina yaki da cin hanci ko ta yi rauni a kan yakin da ta ce yaki ne na ceto kasar nan.
Ya koka kan yadda wasu rubuce-rubuce da wasu ke daukar nauyinsu suka fara bayyana a kafafen sadarwar intanet da jaridu domin sukar gwamnati kan yakinta da cin hanci da rashawa.
“Babu wata suka daga jaridu ko wasu da za su dakatar da yakin. Masu yin sharhi da masu kage a rubuce-rubuce za su yi ta yin aikin banza a kokarinsu na dakatar da jirgin yaki da cin hanci da rashawa,” inji Alhaji Lai Mohammed
Ya kara da cewa: “Lokacin da na gana da Editocin Labarai da Editocin Labaran Siyasa a Legas a ranar Lahadi, na gaya musu cewa gwamnati tana sane da cewa a yayin yaki da cin hanci da rashawa, rashawar za ta mayar da martani. Kuma n ace wadanda suka sace dukiyarmu suka mayar da mu fanko suna da karfi. Suna da gidajen jaridu da rediyo da talabijin da kafofin sadarwar intanet tare da dimbin magoya baya da za su ci gaba da sukar yaki da cin hanci na gwamnati.”
Ya ce “Abin da nake son gaya muku a yau, tunic in hanci da rashawa ya fara mayar da martani. Rubuce-rubucen da ake daukar nauyinsu sun fara bayyana a jaridu da kafafen sadarwar intanet, yayin da wasu suka fara surutai a gidajen talabijin da rediyo domin sukar yaki da cin hanci da kuma wannan gwamnati.”
Don haka sai ya bukaci ’yan Najeriya da kadasu yarda wannan dabara ta masu zame kafar wannan yaki ta ruda su, inda ya ce hatta a kasar Amurka sun gamsu da salon yaki da cin hanci na gwamnatin, inda Sakatariyar Harkokin cikin gidan Amurka ta ambaci hakan a jawabinta wajen taron tattalin arziki na duniya (WEF) da aka gudanar a Dabos ta kasar Switserland.