Za mu murkushe duk wani yunkurin wargaza kasar nan – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin yin amfani da dukkan albarkatun da kasar nan ke da su wajen murkushe duk wani yunkuri na wargaza kasar nan.Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a Katsina, a ranar Litinin da ta gabata lokacin da ya kan ziyarar girmamawa ga Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir […]

Za mu murkushe duk wani yunkurin wargaza kasar nan – Buhari
Za mu murkushe duk wani yunkurin wargaza kasar nan – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin yin amfani da dukkan albarkatun da kasar nan ke da su wajen murkushe duk wani yunkuri na wargaza kasar nan.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a Katsina, a ranar Litinin da ta gabata lokacin da ya kan ziyarar girmamawa ga Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman a fadarsa, inda ya ce kasar nan ta fafata Yakin Basasa da ya hallaka mutum miliyan biyu domin tabbatar da dunkulewarta.
Shugaba Buhari, wanda ya je Katsina don bude Taron Tattalin Arziki da Zuba Jari da aka gudanar yana aikewa da gargadi ne ga wata kungiyar neman kasar Biyafara mai suna kungiyar Al’ummar kasar Biyafara (IPOB) ya ce zai fi zama alheri ga daukacin kasar nan ta yi kunar bakin wake da ta bar irin wannan kamfe ya samu nasara.
Ya bayyana mass fafutikar da “kananan yara” da ba a haife sub a lokacin Yakin Basasar. Shugaba Buhari ya ce: “Yau Najeriya ta kara karfi tare da zama hadaddiyar kasa mai ’yanci ne saboda wadansu mutane sun sadaukar da rayukansu domin amfanin kasar. Akalla mutum miliyan biyu suka rasu a lokacin Yakin Basasar, amma yau wadansu mutanen da ba a haife su lokacin Yakin Basasar ba, suna fafutikar neman raba kasar nan. Ba za mu bari hakan ya faru ba.”
Sai Shugaba Buhari ya bukaci ’yan Najeriya kan su kara hakuri da gwamnatinsa, saboda a cewarsa wahalar da ake ciki a yanzu ba za ta rasa nasaba da kokarin aza harsashin dora kasar nan a turbar ci gaba ba.
Da yake magana kan tattalin arziki Shugaba Buhari ya nuna takaicinsa kan faduwar farashin man fetur, inda ya ce a lokacin da ya karbi mulki a ranar 29 ga Mayun bara farashin man fetur ya fadi kasa zuwa Dala 30, sabanin yadda ake sayarwa a shekara 16 na gwamnatin PDP. “Ba za mu ci amanar da ’yan Najeriya suka dora mana ba, kuma za mu tabbatar da cewa jami’an gwamnati suna yin aiki don amfanin kasa,” inji shi. Da yake mayar da jawabi Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta sake dawo da makarantun kwana da kuma kwalejojin horar da malamai domin samar da kwararun malamai.
Ya ce, “Makarantun horar da malamai sun taimaka wajen samar da kwararrun malamai, amma a yanzu, malamai marasa kwarewa ne suke koyarwa a makarantunmu.”
Sarkin ya kara da cewa, a shekarun baya makarantun kwana sun taimaka wajen samar da da’a a tsakanin dalibai ta yadda suka taso baligai masu sanin ya kamata.