Za mu rage farashin siminti zuwa N3,500 — BUA
Za mu kara gina wasu kamfanonin sarrafa siminti guda biyu.
Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdul-Samad Rabiu, ya ce kamfaninsa zai rage farashin siminti zuwa naira 3,500 a Najeriya.
Abdul-Samad Rabiu ya bayyana haka ne ga manema labarai a fadar shugaban Najeriya, jim kadan bayan ganawarsa da shugaba Tinubu ranar Juma’a da maraice.
- Cibiyar Binciken Aikin Gona ta soma bikin cika shekara 100 da dashen itatuwa
- Gwamnatin Obasanjo ta fi kowacce bunkasa tattalin arzikin Najeriya — El-Rufai
Ya ce ya dauki matakin rage farashin simintin ne a wani yunkuri na mara wa gwamnatin Tinubu baya wajen daidaita farashin muhimman kayayyaki a kasar
Abdul-Samad Rabiu ya kuma ce kamfaninsa zai kara gina wasu sabbin kamfanonin sarrafa siminti biyu a karshen shekara ko farkon shekara mai zuwa.
Ya ce kamfanonin wadanda shugaban kasar zai kaddamar idan sun kammala, za su sanya kamfanin ya rika samar da metric tan miliyan 17 na siminti.
A cewarsa, hakan zai sa Kamfanin ya rage farashin siminti zuwa naira 3,500 a kowane buhu.