Za mu ranto Naira tiriliyan 9 domin cike giɓin Kasafin Kuɗin 2025 — Gwamnatin Tarayya
Ministan ya ce kasafin kuɗin ya ƙunshi manyan ayyuka da kuma na musamman da za a gudanar a faɗin ƙasar.
Majalisar Zartaswar Najeriya ta sanar da shrinta na karɓo rancen aƙalla Naira tiriliyan 9 domin cike giɓin Kasafin Kuɗin shekarar 2025.
Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsaren Tattalin Arziki, Atiku Bagudu ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema labarai a ranar Alhamis.
- Zanga-zanga: A cikin gida aka kama ’ya’yanmu aka kai kurkuku —Iyaye
- Yau wa’addin girbi da Lakurawa suka ba manoman Sakkwato ke karewa
Aminiya ta ruwaito cewa Majalisar Zartarwar ta amince da kasafin kuɗin na 2025 da ya kai naira tiriliyan 47.9.
Da yake yi wa manema labarai jawabi bayan kammala taron majalisar da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta, Ministan ya ce kasafin kuɗin ya ƙunshi manyan ayyuka da kuma na musamman da za a gudanar a faɗin ƙasar.
“Mun amince da kasafin kuɗin, kuma za a miƙa shi gaban majalisar dokoki ta ƙasa domin yin nazari da kuma amincewa da shi,” in ji Bagudu.
“Za a ciyo sabon rancen da ya kai naira tiriliyan 9.2 don cike giɓin kasafin kuɗin na shekarar 2025.
Ya ce an yi hasashen samun bunƙasar yawan kayayyakin da ake samarwa a cikin gida da kashi 4.6 cikin 100.