Za mu riƙe albashin likitocin da ke yajin aiki — Gwamnati

Za mu aiwatar da dokar babu aiki babu albashi kamar yadda Dokar Ƙwadago ta tanada.

Za mu riƙe albashin likitocin da ke yajin aiki — Gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta yi barazanar riƙe albashin likitocin da suka tsunduma yajin aiki a wannan makon.

Gwamnatin ta yi barazanar ce yayin da take bayyana rashin jin daɗinta kan matakin da ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta Nijeriya, NARD ta ɗauka na fara yajin aikin gargaɗi na kwana bakwai, duk da ƙoƙarin take yi na share musu hawaye.

A wata sanarwa da Kakakin Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, Ado Bako, ya fitar, ya ce gwamnatin ta sanar da aiwatar da dokar “ba aiki, babu albashi” na tsawon kwanakin da likitocin suka ɗauka suna yajin aikin kamar yadda Dokar Ƙwadago ta tanada.

Bako ya bayyana cewa wannan matakin ba ya nufin an yi watsi da halascin damuwar likitocin, sai dai yana nufin tabbatar da cewa muhimman ayyukan kiwon lafiya sun ci gaba da ɗorewa ba tare da samun wata katsewa ba saboda amfanin al’umma.

Ana iya tuna cewa dai likitocin sun fara yajin aikin ne a ranar Litinin, domin yi gwamnati matsin lambar ceto wata abokiyar aikinsu, Dokta Ganiyat Popoola da ke hannun masu garkuwa da mutane tun cikin watan Disambar shekarar da ta gabata.

Bako ya ƙara da cewa, ma’aikatar tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro, sun dukufa wajen ganin an sako Dakta Popoola, kuma a halin da ake ciki, akwai tattaunawa mai ƙarfi da ake yi don ganin a kuɓutar da ita daga hannun masu garkuwa da mutanen.

Ma’aikatar ta buƙaci likitocin da su koma kan teburin tattaunawa, inda ta jaddada muhimmancin samar da haɗin kai da kuma dawwamammen mafita kan ƙalubalen da ke fuskantar fannin kiwon lafiya a Nijeriya.

Sanarwar ta sake jaddada aniyar ma’aikatar na gudanar da tattaunawa mai ma’ana da kuma yin aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki domin cimma maslaha mai ɗorewa.