Za mu rufe duk gidan man da ya sayar da mai sama da farashin gwamnati – Hukumar DPR
Cif Caesar Douglas shi ne Shugaban Hukumar kula da Albarkatun man fetur (DPR) na Shiyar Jos. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu ya bayyana ayyukan wannan hukuma tare da bada tabbacin cewa daga yanzu ba za su taba barin wani gidan mai a kasar nan ya sayar da mai sama da farashin da […]

Cif Caesar Douglas shi ne Shugaban Hukumar kula da Albarkatun man fetur (DPR) na Shiyar Jos. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu ya bayyana ayyukan wannan hukuma tare da bada tabbacin cewa daga yanzu ba za su taba barin wani gidan mai a kasar nan ya sayar da mai sama da farashin da gwamnati ta ce a sayar ba. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Aminiya: meye ayyukan wannan hukuma?
Cif Douglas: Ayyukan wannan hukuma sune, tabbatar da cewa masu kasuwancin man fetur suna bin ka’idoji a harkokin kasuwancin mai. Wato masu harkokin mai idan za su gina gidan mai su nemi lasisi daga wajenmu domin su sayar da man.
Kuma aikin wannan hukuma, ba ya tsaya ne kan gidajen mai kadai ba. Ayyukan wannan hukuma ya hada har da binciken mai da hako mai da kuma tatar mai, muna sa ido domin mu tabbatar an bi ka’idoji wajen gudanar da wadannan ayyuka. Don haka ake ganinmu a duk inda ake harkokin mai.
Kamar yadda muka ce, doka ta ce idan za ka yi harkokin sayar da mai, ya kamata ka samu izini. Don haka masu bude gidajen mai ba tare da lasisi ba, suna cutar gwamnati. Kuma gwamnati tana ba da tallafi domin al’ummar Nijeriya su samu man a cikin sauki. Don haka masu bude gidajen mai ba tare da lasisi ba, ba tare da biyan haraji ba, kuma suna sayar da man ba kan farashin gwamnati ba, doka ta ba mu damar mu rufe irin wadannan gidajen mai. Don haka muka ce ba za mu bar duk wani gidan mai da ba shi da lasisi ba ya sayar da mai.
Kuma aikin wannan hukuma ne ta tabbatar man da aka bayar ya kai inda aka ce a kai, kuma ta tabbatar an sayar da shi kan farashin gwamnati. Don haka a duk lokacin da aka kawo mai, mu kan je mu bincika mu tabbatar an kai man nan inda aka ce a kai kuma an sayar da shi kan farashin gwamnati.
Aminiya: Wanne hali ake ciki dangane da gidajen mai guda 23 da kuka rufa a jihar nan ta Filato?
Cif Caesar Douglas: Gidajen man da muka rufe za su cigaba da zama a rufe. Duk gidan man da yake da mai a lokacin da muka rufe wadannan gidajen mai, mun sa an sayar da man kan farashin gwamnati na naira 87. Bayan haka sun biya tarar da muka yi masu. Dama dokarmu ta ce idan aka kama gidan mai yana sayar da mai kan farashi sama da farashin gwamnati, mu sayar da man kan farashin gwamnati mu sanya tara sannan kuma mu rufe gidan man har zuwa watanni biyu. Domin ya zama darasi ga sauran gidajen mai.
Aminiya: Wanne sako ko kira ne kake da shi zuwa ga duk masu gidajen mai?
Cif Caesar Douglas: Abin da zance wa masu gidajen mai shi ne, su bi ka’ida ta hanyar sayar da mai kan farashin gwamnati. Kuma man nan idan ba an je Legas ko Kalaba ko Warri an dauko wannan mai ba gwamnati ba za ta dauko ba. Amma idan mutum ya san zai je Legas ko Kalaba ko Warri ya dauko mai ya zo nan Arewa ba tare da ya sayar kan farashin gwamnati ba, to ya huta. Domin mu idan ka kawo wannan mai mu za mu tsaya mu tabbatar ka sayar da man nan kan farashin gwamnati. Domin gwamnati ba ta ce mana an kara farashin mai ba, kuma mu mun san farashin mai da Depot-Depot na kasar nan suke sayar wa masu gidajen mai shi ne Naira 77 da kwabo 66. Amma idan akwai wani mai gidan mai da ya ce ya sayi mai sama da haka ya zo ya yi mana bayani, mu za mu bi masa hakkinsa. Domin ko a makon da ya gabata Daraktan DPR na kasa ya rufe wadansu Depot-Depot da suka ajiye mai ba tare da sun sayar wa jama’a.