Za Mu Rufe Jami’o’i Nan Da Kwanaki Bakwai —SSANU 

Ma’aikatan jami’o’in Najeriya sun yi barazanar shiga yajin aiki idan gwamnati ta ki biyan bukatunsu cikin mako guda

Za Mu Rufe Jami’o’i Nan Da Kwanaki Bakwai —SSANU 

Shugaban Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU) Mohammed Ibrahim ya ce za su tafi yajin aiki idan gwamnati ta ki biya musu bukatunsu nan da kwanaki bakwai.

Ya bayyana cewa za su shiga yajin aikin ne tare da wasu kungiyoyin ma’aikatan jami’o’i biyu na kasar nan

Ibrahim ya ce, sun ba Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki bakwai, daga ranar Litinin 4 ga Mayu, 2024

Da ake hira da shi a gidan talabijin na Channels TV ranar Lahadi, ya yi barazanar cewa kungiyoyin za su rufe jami’o’in gaba daya, idan gwamnatin ba ta yi wani abu ba a karshen wa’adin.

“Mu ne masu kula da harkokin tsaron jami’o’in da gudanar da mulki da kula da likitoci da dakunan kwanan dalibai da da wutar lantarki da tafiyar da komai bayan koyarwa, don haka da zarar mambobinmu sun daina aiki, babu wata jami’a da za ta iya aiki a Najeriya.

Tinubu zai tafi Faransa daga nan ya zarce Habasha

NAHCON ta tsawaita wa’adin biyan kuɗin Hajjin bana

Jami’ar ABU da ke Zariya ta yi sabon shugaba

An soma rigimar haraji tsakanin China da Amurka