Za mu sa Gwamna Jang ya dawo da kudin al’ummar Filato – Lalong

Mista Simon Lalong wanda ya shugabancin Majalisar Dokokin Jihar Filato a lokacin tsohon Gwamna Joshua Dariye shi ne dan takarar Gwamnan Jihar a karkashin Jam’iyyar APC. A tattaunawar da ya yi da wakilinmu ya ce a cikin shekara takwas da Gwamna Jonah Jang ya yi yana mulkin Jihar Filato, ya yi almubazaranci da kudin jihar. […]

Za mu sa Gwamna Jang ya dawo da kudin al’ummar Filato – Lalong
Za mu sa Gwamna Jang ya dawo da kudin al’ummar Filato – Lalong

Mista Simon Lalong wanda ya shugabancin Majalisar Dokokin Jihar Filato a lokacin tsohon Gwamna Joshua Dariye shi ne dan takarar Gwamnan Jihar a karkashin Jam’iyyar APC. A tattaunawar da ya yi da wakilinmu ya ce a cikin shekara takwas da Gwamna Jonah Jang ya yi yana mulkin Jihar Filato, ya yi almubazaranci da kudin jihar. Don haka ya ce idan ya zama Gwamna zai sanya ya dawo da kudin jihar da ya kwashe ba bisa ka’ida ba:

Aminiya: Mene ne kudurinka game da takarar kujerar Gwamnan Jihar Filato da kake yi karkashin Jam’iyyar APC?
Simon Lalong: To, babban kudurina kan wannan takara da nake yi, shi ne na kawo canji a Jihar Filato. Musamman ganin irin miyagun abubuwan da gwamnatin jihar karkashin Gwamna Jonah Jang ta tafka. Ya zama wajibi a gare mu mu tashi mu kawo canji a jihar nan, domin mu ceto jihar daga mawuyacin halin da ta shiga sakamakon irin wadannan miyagun abubuwa.
Aminiya: Wadanne irin miyagun abubuwa ne kake ganin gwamnatin Jonah Jang ta aikata a cikin shekara takwas da ta yi tana mulkin Jihar Filato?
Simon Lalong: A gaskiya gwamnatin Jonah Jang ta aikata miyagun abubuwa da dama a jihar nan, a cikin shekara takwas da ta yi tana mulkin jihar nan. Ka ga dai na farko ta jefa jihar nan a cikin rikice-rikice wanda ya yi sanadin asarar dubban rayukan al’umma tare da dukiyoyi na biliyoyin Naira.
Haka kuma gwamnatin nan ta kasa biyan albashin ma’aikatan jiha da malaman makarantun firamare da malaman manyan makarantun jihar da ’yan fansho dukkansu sun yi wata da watanni babu albashi.
Hatta ’yan majalisar dokokin jihar nan sun yi wata shida ba a biya su albashi ba, don haka babu wani wakilci nagari da suke yi wa al’ummar Jihar Filato a majalisar dokokin. Sakamakon wannan al’amari na rashin biyan albashi a jihar nan, duk abubuwa sun tabarbare don haka mutanen jihar suna cikin wahala.
Har ila yau a shekara takwas da gwamnatin Jang ta yi tana mulkin jihar nan, ta gina Gidan Gwamna har guda hudu, bayan Gidan Gwamnan da ake da shi a jihar. Na farko Gwamna Jang ya debi makudan kudi ya kashe wajen gyara gidansa ya mayar da shi kamar gidan gwamnatin jihar, haka kuma ya zo ya sake kashe wasu makudan kudi wajen gyara ofishin Mataimakin Gwamnan jihar da ke Tudun Wada ya mayar da shi kamar gidan gwamnati, ya kuma dauki wannan gida ya mayar da shi fadar Gbong Gwom Jos. Kuma ya je ya sake gina wani sabon Gidan Gwamna a kauyen Du. Wannan ba karamin almubazaranci aka yi da kudin al’ummar Jihar Filato domin ba gidajen Gwamna al’ummar Filato suke bukata ba.
Bayan haka gwamnatin jihar ta ciwo basussuka daga bankuna da dama a nan gida Najeriya da kasashen waje. Basussukan da gwamnatin nan take son ta bari sun kai kusan Naira biliyan 400. Gwamnatin Jonah Jang ta ciwo bashi daga bankin Musulunci har Naira biliyan tara. An ciwo basussuka da sunan wai ana yin hanyoyi a jihar nan, bayan mun san a cikin hanyoyin akwai hanyoyin Gwamnatin Tarayya wadanda ita ce ta biya kudin da aka yi su. Dubi abin da gwamnatin jihar nan ta yi kan kudin rage radadin talauci na SURE-P, wadanda sun kai Naira biliyan 81. Wadannan kudi an bayar da su ne domin a samar wa matasan jihar nan ayyukan yi. Amma sai gwamnatin ta ki ta yi bayani kan yadda ta yi amfani da kudaden.
’Yan majalisar jihar nan sun yi kokarin bincike kan wadannan kudade na SURE-P amma sai dan Gwamnan ya yi karar majalisar a kotu kan ta dakatar da majalisa kan wannan kokari da ta yi na binciken maganar.
Bayan haka a dukkan jihohin Najeriya 36, a Jihar Filato ne kadai Gwamna ya nada dansa a matsayin Kwamishinan Ma’aikatar Filaye da Safiyo kuma ya nada shi a matsayin mai ba shi shawara kan ayyuka na musamman.
Aminiya: Irin bayanin da ka yi za ka binciki gwamnatin ta Jonah Jang ke nan, idan ka zama Gwamna?
Simon Lalong: To, kamar yadda dan takarar Shugaban kasarmu Janar Muhammad Buhari ya ce zai, yi na jan layi kan abubuwan da aka aikata a Najeriya, ni ma haka zan yi. Domin ya ce zai ja layi ne kan abubuwan da aka aikata, ba zai kulle kowa ba, amma ya ce duk wanda ya kwashi kudin al’umma dole zai dawo da su. Don haka ni ma ba zan binciki Jang ba, amma za mu ja layi mu sanya ya dawo da duk kudin al’ummar Jihar Filato da ya kwasa ba bisa ka’ida ba.
Aminiya: To, wace manufa kake da ita ga jihar nan?
Simon Lalong: Manufarmu ta farko a jihar nan ita ce samar da tsaro. A wannan bangare za mu kafa majalisar dattawa ta musamman wadda za ta rika ba mu shawarwari, domin babban burinmu shi ne mu hada kan al’ummar jihar nan. Muna ganin idan muka yi haka za a samu tabbataccen zaman lafiya a jihar.
Za mu kuma bunkasa harkokin ilimi da kiwon lafiya da noma da harkokin kasuwanci. Kan maganar bunkasa harkokin kasuwanci, za mu sake gina babbar kasuwar Jos da ta kone don mu samu hanyoyin samun kudin shiga a jihar nan. Za mu bunkasa harkokin yawon bude ido musamman ganin sunan da jihar ta yi a wannan bangare na yawon bude a Najeriya.
Aminiya: Me za ka ce kan korafin da Jam’iyyar PDP ke yi kan amfani da na’urar tantance masu zabe, da Hukumar INEC ta ce za ta yi amfani da ita a zabe?
Simon Lalong: To, wannan ya nuna cewa Jam’iyyar PDP ta zama jam’iyyar adawa a Najeriya, domin ita ce take ta koke-koke kan tsarin zabe na amfani da na’urar tantance masu zabe da Hukumar INEC ta ce
za ta yi. Wannan na’urar tantance masu zabe, za a yi amfani da ita ce domin a samu zabe mai kyau wanda babu magudi a cikinsa. An yi amfani da wannan na’ura a kasashen Ghana da Senegal da Saliyo da
Afirka ta Kudu kuma an samu gagarumar nasara. Wannan na’ura wata hanya ce ta ceto al’ummar Najeriya daga magudin zabe.