Za mu sa ido a kan tubabbun – Gwamnatin Kano
A makon jiya ne gwamnatin Jihar Kano ta yi wa wasu barayin shanu su 39 afuwa wadanda suka mika kansu tare da makamansu ga gwamnati.Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya karbi wadanann tubabbu ne da suka fito daga garin Gomo a yankin karamar Hukumar Sumaila cikin Jihar Kano, daga wurin Kwamishinan ‘Yan sandan jihar […]

A makon jiya ne gwamnatin Jihar Kano ta yi wa wasu barayin shanu su 39 afuwa wadanda suka mika kansu tare da makamansu ga gwamnati.
Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya karbi wadanann tubabbu ne da suka fito daga garin Gomo a yankin karamar Hukumar Sumaila cikin Jihar Kano, daga wurin Kwamishinan ‘Yan sandan jihar Muhammad Musa Katsina.
A lokacin da yake karbar tubabbun, Gwamna Ganduje ya bayyana cewa sun samu nasarar yakin da suke yi tsakaninisu da barayin shanu a jihar, “mun fara samun nasara a yakin da muke yi tsakaninmu da barayin shanu a jihar nan. Da taimakon jami’an tsaro in sha Allah za mu ci gaba da samun nasara. Tun daga lokacin da muka daura wanann yaki zuwa yanzu mun kama barayin shanu sama da 253 haka kuma mutum 11 sun rasa ransu a gumurzun yakin namu.”
Gwaman Ganduje ya kara da cewa, tun daga wannan lokaci gwamnati ta karbo kimanin shanu dubu 4 da awaki da tumaki kimanin dubu daya. Haka kuma an gano rakuma 11 da jakuna 19 da kaji guda 9.
A cewar Gwamnan, tuni gwamnatin ta kafa kwamiti wanda aka dora masa alhakin mayar da dabbobin ga masu shi, wanda tuni kwamitin ya mayar da fiye da rabin dabbobin ga masu su na ainihi.
Dama dai tun a watan Disambar bara Gwamnan ya bayar da sanarwar cewa gwamnati za ta yi afuwa ga duk wani barawon shanu da ya mika kansa ya daina satar.
Da yake bayani game da matakin da gwamnati za ta dauka don ganin tubabbun barayin ba su yi tuban muzuru ba, Daraktan watsa labarai na Gwamnan Kano Baba Halilu dantiye, ya bayyana cewa tunda su suka kawo kansu suka kuma nuna nadamarsu, to ko a addinin Musulunci ya kamata a saurare su a karbi tubansu. “A addinin Musulunci duk wanda yake aikata wani laifi idan ya tuba ya wajaba ka karbi tubansa, ma’ana ka yarda da tubansa. Ba ka da hujjar da za ka karyata tubansa, matukar ba ya koma aikata wanann laifi ba. Don haka lokacin da wadanann mutane suka kawo kansu gwamnati ta karbi tubansu tare da yi musu kyakkyawan zato. “Inji shi.
Haka kuma Daraktan watsa labaran ya bayyana cewa dama tunda farko gwamnatin ta hannun Ma’aikatar Shari’a ta jihar ta tsara wani fam da aka ba wa kowane daya daga cikinsu ya sanya hannu a kai cewa ya yi tuba na gaskiya. “Ma’aikatar Shari’a ta ba wadannan tubabbu fam inda kowanensu ya cika ya kuma sanya hannu a kai. Wanda mu a wurinmu wanann sanya hannun da suka yi muke daukarsu a matsayin rantsuwa tare da alkawarin ba za su koma ga aikata laifinsu ba. “
Baba dantiye ya kara da cewa, “Bayan gwamnatin ta karbi tubansu sai kuma ta yi alkawarin taimaka musu da dan wani abu da za su yi sana’a da shi. Ba wai tsabar kudi gwamnati za ta ba su ba, za ta taimaka musu ne game da sana’o’in da suke yi tun farko. Misali manomi ko makiyayi za a taimaka masa da abin da zai inganta sana’arsa. Duk mutumin da ka dauki abu, musmman na jari ka ba shi, ai kai ma ba za ka kyale shi ya tafi haka sakil ba, dole za ka rika bibiyarsa don sanin me yake ciki.
Kada a manta muna da bayanan kowannensu haka kuma al’ummar da suke zaune a cikinsu mutanensu ne don haka sun sansu, sun kuma san halin da suke ciki. Da zaran wani abu ya faru za mu iya sani babu abin da zai buya mana.”
A cewar dantiye idan har aka samu su (tubabbun) sun sake aikata irin wannan laifi a nan gaba, ‘’to su ma sun san babu batun afuwa, sunansu masu laifi kai tsaye. Za kuma a yi musu hukunci mai tsananin gaske saboda karya alkawari da suka yi.”