‘Za mu sa jirage marasa matuka a yaki da ’yan bindiga’
Za kuma a karo jirage takwas da masu saukar ungulu domin murkushe ‘yan bindiga
Shugaban Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar
Rundunar Sojin Sama ta Najeriya za ta yi amfani da jirage marasa matuka wurin yakar ’yan bindiga a yankin Arewa ta Yamma da ta tsakiya.
Shugaban Rundunar, Air Marshal Sadique Abubakar ya ce na gaba za a tura jirage marasa matuka guda takwas jihohin Zamfara Katsina da Gombe da ’yan bindiga ke addaba.
A ziyararsa ta ganin irin nasarar da ake samu a yaki da mahara a Jihar Katsina, Air Mashal Sadique ya ce dakarun rundunar guda 71 da za su rika kula da jiragen da ke samun horo a China na gab da dawowa gida.
Ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya za ta karo jirage takwas da masu saukar ungulu da karin kayan yaki domin murkushe ayyukan mahara a yankin.
Shugaban Rundunar ya shaida wa ’yan jarida cewa an yi nasarar ragargaza sansanonin bata-garin a Jihohin Katsina, Zamfara, Neja da kuma Sakkwato.
Ya ce gwamnati ta dukufa wajen ganin an samu aminci a yankunan da ke fama da matsalar tsaro a yankin.
Sadique ya ce ba za su kakkauta ba wajen ragargazar mahara da sauran masu aikata manyan laifuka ba saboda a yi saurin kawar da ayyukansu.