Za mu saka wa nakasassun Jihar Osun da alheri – Gwamna Rauf Aregbesola
Gwamnan Jihar Osun, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya bayyana aniyar gwamnatinsa ta saka wa nakasassun jiharsa da alheri, inda ya ce, gwamnatinsa ba ta yi wani shiri na korar nakasassun mabarata daga Jihar ba, domin su ma mutane ne kamar kowa kuma ‘yan Najeriya ne da suke da ‘yancin gudanar da al’amuransu a ko’ina cikin kasar […]
Gwamnan Jihar Osun, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya bayyana aniyar gwamnatinsa ta saka wa nakasassun jiharsa da alheri, inda ya ce, gwamnatinsa ba ta yi wani shiri na korar nakasassun mabarata daga Jihar ba, domin su ma mutane ne kamar kowa kuma ‘yan Najeriya ne da suke da ‘yancin gudanar da al’amuransu a ko’ina cikin kasar nan kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar. Ya ce, a maimakon korar irin wadannan mutane Gwamnatinsa za ta hada kai da Gwamnatin Tarayya ne domin tabbatar da ganin shirin bude makarantun almajirai na kasa baki daya ya kankama a jihar.
Gwamnan ya fadi haka ne a ranar Juma’a da ta wuce cikin jawabin da ya yi wa daruruwan nakasassun maza da mata a wata ganawa, tare da shirya musu liyafar cin abinci a karo na farko a cikin gidan gwamnati a birnin Osogbo, hedkwatar Jihar Osun.
Gwamnan wanda yake tare da Uwargidansa Hajiya Sherifat Abidemi Aregbesola da mataimakiyarsa Uwargida Grace Titi Laoye Tomori, da wasu kusoshin gwamnati, sun gwamutsa da makafi da guragu suka yi ta cashewa da raye-raye na wakoki da kide-kiden Hausawa da aka shafe fiye da awoyi biyu ana yi a wannan wuri.
A hirar da Gwamna Rauf Aregbesola ya yi da wakilinmu jim kadan bayan kammala ganawar da yayi da wadannan nakasassun mutane, ya ce, “muhimman abubuwa guda biyu ne yasa muka gayyaci wadannan ‘yan uwa na mu zuwa gidan gwamnati. Abu na farko shi ne, mafi yawancinsu sun jefa wa jam’iyya ta APC kuri’u a zaben 9 ga watan Agusta da ya gabata, wanda muka yi nasara a nan Jihar Osun. Wannan wata hanya ce da muke so mu nuna masu farin cikinmu a dalilin soyayya da kauna da gaskiya da suka nuna mana. Abu na biyu shi ne, mu nuna masu cewa, a matsayinsu na ‘yan kasar Najeriya muna matukar bukatar goyon bayansu musamman ta fannin tsaro da muke fatan za su kasance a shirye wajen hanzarta ba mu labarin bullar wani sabon abun da basu amince da shi ba. Za su iya ba mu irin wannan labarai ne ta hannun jagoran su wato, Sarkin Hausawa.”
“Ya kamata mu nuna godiyarmu gare su (nakasassu) a dalilin goyon baya da suka ba mu kuma, mu karfafa musu guiwar ci gaba da yin hakan tare da neman gudunmawarsu ga al’amuran da suka shafi tsaro domin samun zama lafiya da kwanciyar hankali a wannan jiha.” Inji shi.
A kan batun makarantun koyar almajirai da Gwamnatin Tarayya ta fara ginawa a wasu jihohi, sai Gwamnan yace, “yanzu haka muna yin aikin hadin guiwa da Gwamnatin Tarayya domin gano ainihin wurin da ya dace da gina irin wannan makaranta da samar da malamai tare da goyon bayanmu ga shirin ilmantar da makiyaya na kasa.”
Dangane da dangantakar gwamnatinsa da al’ummar Arewacin kasa dake zaune a jihar, sai Gwamna Aregbesola, ya ce: “Ya kamata su rika kallon kansu a matsayin ‘yan uwanmu domin su ma ‘yan jihar Osun ne, tare muke babu abin da zai raba mu, kuma babu wanda zai takura musu. Ku saki jiki domin mu hadu mu samar da abubuwan da za su kawo ci gaban al’umma da kananan hukumomi da wannan jiha da za mu samo hanyar hada kan dunkulalliyar Najeriya da ci gaban da zai kaita shiga cikin jerin kasashen duniya da suka ci gaba.”
Da wakilinmu ya karkata tambayoyi ga Mataimakiyar Gwamna a Jihar Osun, Uwargida Grace Titi Laoye Tomori, cewa ta yi, “ina matukar farin ciki da ganin wadannan mutane maza da mata da kananan yara, shi ne yasa ka ga ina taka rawa da yin guda a tare da su. Muna so su sani cewa, su ma suna daga cikinmu babu bambanci a tsakanin mu da su babu bambanci tsakanin ‘ya’yansu da na mu ‘ya’yan dukkanmu daya ne.”
“Idan ka tuna Gwamna Rauf Aregbesola ne kadai ya fito fili ya nuna kauna da soyayyar wadannan mutane da janyo su a jiki. Babu wani gwamna ko wata Gwamnatin Jiha a Najeriya da ta taba yin irin haka ga wadannan mutane (nakasassu), Gwamna Aregbesola ne kadai yayi hakan kuma ya aikata hakan ne tsakaninsa da Allah. Akwai muhimman abubuwa da aka yi musu tanadi domin kyautata rayuwarsu a nan gaba,” in ji ta.
Cikin jawabinsa Sarkin makafin Jihar Osun, Ajhaji Idris Isa, wanda ya jagoranci daruruwan nakasassun mutane zuwa wajen ganawa da Gwamnan, ya shaida wa mahalarta taron cewa: “Babu abin da za mu fada da ya wuce addu’ar rokon Allah (SWT) ya kare Gwamnan daga kulle kullen makirci da hassada da makiyansa ke yi. Muna kara rokon Allah ya yi masa sakayya da alheri, ya kare Jihar Osun kuma ya zaunar da kasarmu Najeriya lafiya. Tun daga lokacin da Gwamna Aregbesola ya kama ragamar mulki a Jihar Osun muke yi masa addu’o’in rokon Allah yayi masa maganin dukkan abun da yake damunsa kuma za mu ci gaba da yin irin wadannan addu’o’i gare shi domin mun fahimci cewa, mutum ne mai son jama’a da taimaka wa gajiyayyu kamar yadda yake yi mana ba tare da bambancin kabila ko addini ba. Ya kamata sauran Gwamnoni suyi koyi da shi.”
Da yake amsa wasu tambayoyi daga wakilinmu, Sarkin makafi Idris Isa, mai kimanin shekaru 70 da haihuwa cewa ya yi, “a rayuwata ban taba ganin abun da ya faranta mani rai kamar na yau juma’a da Gwamna ya gayyace mu domin ganawa da shi ba. A baya, babu wani Gwamna da ya taba karrama mu kuma ya san darajarmu tare da janyo mu a jiki kamar wannan Gwamna da yake mulki a yanzu. Abin da ya yi mana a yau, ya kawar da fargabar korarmu daga Jihar Osun da ake yi mishi karya ta hanyar yada jita jitar gwamnatinsa za tayi. Yau dai mun gane cewa, dodorido ake yi mana mun gano gaskiyar komai. A kan maganar tsaro da ya nemi goyon baya da hadin kanmu, ina tabbatar maka cewa, tun tuni muka fara zama da ‘yan majalisa ta muke tattauna wa a kan irin gudunmuwar da za mu bayar domin samun zama lafiya da kwanciyar hankali a wannan jiha da kasa baki daya.”
Shi kuwa Mai ba Gwamna shawara na musamman a kan al’ummomin Arewa mazauna jihar Osun Imam Muhammed Bashir, cewa yayi “a cikin shekaru hudu da Gwamna Aregbesola ya yi a kan mulki ya bayar da umarnin samar da guraben aiki ga yaranmu fiye da 400 da aka dauke su aiki a karkashin hukumar Jihar Osun taTalalfawarayuwar matasa, wato a Ingilishi, “State Youth Empowerment Scheem (OYES)” da suke gudanar da ayyukansu a sassa daban-daban na jihar kuma ake biyansu cikakken albashi kamar sauran matasa ‘yan uwansu. Shi ne ya daukaka martabar Sarakunan Hausawa da yake yin taro da su a kai,a kai, domin jin shawarwarinsu a kan abubuwan da za su kawo ci gaba a jihar. Ba mu taba samun irin wannan garabasa a tarihin kafuwar Jihar Osun shekaru 23 da wucewa ba. Abin da ya rage mana shi ne, irin gudunmuwar da za mu bayar, musamman ta fannin girmama dokoki da kyautata dangantakarmu da jama’a domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.”