Za mu samar da ayyuka miliyan 2 a fannin ƙirkire-ƙirkire da al’adu — Hannatu Musa
Ministar Ma’aikatar Al’adu da Ƙirƙira ta Nijeriya, Hannatu Musa ta ce tsarin ya yi daidai da manufofin gwamnati mai ci.
Ministar Al’adu da Ƙirƙira, Hannatu Musa Musawa, ta bayyana shirin samar da jarin dalar Amurka biliyan 100 domin samar da ayyuka miliyan biyu a ɓangaren ƙere-ƙere da al’adu domin farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya.
A wata hira da ta yi da manema labarai, Ministar ta ce suna da zummar cimma wannan muradi ne domin ganin an samu kaso mai tsoka a kasuwar duniya na sama da dala tiriliyan 1 a cikin Ma’aikatar Al’adu da Ƙirƙira ta Nijeriya wanda ya yi daidai da manufofin gwamnati mai ci.
- Mutanen gari sun kama mai garkuwa da mutane a Jos
- An ba masu tsoffin gidaje kwana 7 su fice a Ibadan
Musawa ta lura cewa hakan yana yiwuwa tare da damar shiga cikin ƙirƙirar al’adu da ƙimar tattalin arzikin al’adu ta hanyar manufofin ba da damar yanayin kasuwanci.
“A halin yanzu mun haɗa gwiwa da ma’aikatan gwamnati da na masu zaman kansu kuma mun sanya hannu kan yarjejeniya da Ƙungiyar Tattalin Arziki ta Najeriya (NESG) don haɓaka aikin jawo sabbin hanyoyin samar da kuɗaɗe ga masu ƙirƙira” in ji ta.
Ministar ta kuma sanar da kulla haɗin gwiwa da Gidauniyar BigWin, wata babbar abokiyar ci gaban ƙasa da ƙasa, don samar da ayyukan yi da dabarun masana’antu.
A cewar ministar, ma’aikatar ta mayar da hankali ne kan kulla haɗin gwiwa da gidauniyar BigWin la’akari da nasarar da ta samu wajen samar wa matasa ƙasar Rwanda 500,000 ƙwarewa a fasahar zamani domin dogaro da kai da kuma samar da ayyukan yi ga miliyoyi jama’a a ƙasar Cote d’Ivoire.
Musawa ta ci gaba da cewa ma’aikatar tana ƙoƙarin aiwatar da wasu muhimman ayyuka a sassa huɗu domin samar da ayyukan yi miliyan biyu a fannin ƙirƙire-ƙirƙire ta hanyar haɗin gwiwa da BigWin.
“Abu na farko, shi ne kawo dabarun samar da ayyukan yi, dabarun saka hannun jari, haɗin gwiwa, da inganta hanyoyin samun kuɗi da zai bunkasa samar da ayyukan yi,” in ji ta.