Za mu sarrafa dukiyar da ba a san mai ita ba – Saraki

Shugaban Majalisar Dattijai Bukola Saraki, a ranar Larabar da ta gabata ya ce bijiro da kudurin dokar dukiyar da babu masu ita ko suka ki bayyana, za a sarrafata don ayyukan bunkasa kasa. Da yake bude fagen sauraren ra’ayin jama’a kan kudurin, wanda kwmaitin kula da kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya  ta shirya, karkashin […]

Za mu sarrafa dukiyar da ba a san mai ita ba – Saraki

Shugaban Majalisar Dattijai Bukola Saraki, a ranar Larabar da ta gabata ya ce bijiro da kudurin dokar dukiyar da babu masu ita ko suka ki bayyana, za a sarrafata don ayyukan bunkasa kasa.

Da yake bude fagen sauraren ra’ayin jama’a kan kudurin, wanda kwmaitin kula da kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya  ta shirya, karkashin jagorancin Bukar Mustapha, Saraki ya ce amfani da dukiyar zai zaburar da muhimman sassan juya tattalin arziki.

Ya ce tsawon shekaru cibiyoyin hada-hadar kudi a kasar nan suna juya kudin da aka tsibe a asusun ajiya na banki da ba a taba su, tare da ribar da aka samu ta kasuwar hannayen jari.

Saraki wanda ya samu wakilci shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattijai, Santa Philips Aduda, ya ce tabbatar da dokar zai karfafa gwiwa da jan hankali masu sha’awar zuba jaroi a muhimman sassan juya akalar tattalin arzikin Najeriya.

Tun farko a jawabinsa, Mustapha ya ce ribar hannayen jari da masu ita ba su karba ba, an kimanta darajarta da Naira biliyan 104. Ya ce kafa dokar zai bayar da ka’idojin da doka ta tanada don sarrafa dukiyar da babu mai ita ko ba su bayyana ba.

 

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno