Za mu sarrafa kudin inganta Arewa maso Gabas bisa amana – Tumsah

Mataimakin Shugaban Kwamitin Asusun Tallafa wa wadanda ta’addanci ya tarwatsa a yankin Arewa maso Gabas, Alhaji Tijjani Tumsah, ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin a tattara daukacin gudunmawar da aka bayar don sake tsugunar da wadanda ta’addancin ya jikkata a yankin, tare da sarrafa su bisa amana ta yadda za a […]

Za mu sarrafa kudin inganta Arewa maso Gabas bisa amana – Tumsah
Za mu sarrafa kudin inganta Arewa maso Gabas bisa amana – Tumsah

Mataimakin Shugaban Kwamitin Asusun Tallafa wa wadanda ta’addanci ya tarwatsa a yankin Arewa maso Gabas, Alhaji Tijjani Tumsah, ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin a tattara daukacin gudunmawar da aka bayar don sake tsugunar da wadanda ta’addancin ya jikkata a yankin, tare da sarrafa su bisa amana ta yadda za a kyautata rayuwar al’ummar yankin.
Alhaji Tijjani Tumsah ya bayyana haka ne a hirarsa da  Aminiya a Abuja, inda ya ce, za su yi taro a karkashin jagorancin Janar Theophilus danjuma domin fito da tsare-tsaren sake gina garuruwa da samar da kayan inganta rayuwa ta yadda za a sake tsugunar da al’ummar.
Ya ce zai daidaita kokarin da ake yi wajen kyautata yankin, ta yadda ba za a maimaita abin da aka shirya aiwatarwa ba. Ya ce manufar fitar da tsare-tsaren shi ne a tantance duk wani dauki da ake shirin yi, tare da tattara bayanai, al’amarin da ya ce za su zama shirin Shugaba Buhari na inganta yankin Arewa maso Gabas.
A cewar Tumsah, tuni an tara kimanin Naira biliyan 25 daga cikin Naira biliyan 50 da aka alkawarta a wajen kaddamar da asusun, ya ce: “Har yanzu ba a taba kaso mai yawa daga cikin Naira biliyan 25 da aka tara ba, kuma za a yi amfani da kudin yadda waajen kyautata rayuwar al’ummar Arewa maso Gabas.”
Tumsah ya ce, “Kuma za mu bayyana asusun ajiyar da kudin suke, kamar yadda muka saba yi daga lokaci zuwa lokaci, sannan mun dora alhakin kula da asusun a hannun kwararrun masu binciken kudi na KPMG. Komai a bayyane yake karara, duk mai shakka, ya san cewa alkinta wannan dukiya shi ne kudurinmu.”