Za mu sauya fasalin kasuwancin Kano ya koma amfani da fasahohin zamani – GBB
Kamfanin Galaxy Backbone (GBB) mallakin Gwamnatin Tarayya ya ce yana son yin amfanin da hanyoyin fasahar sadarwa na zamani a kasuwannin Jihar Kano. Kamfanin ya ce zai yi hakan ne da nufin sauya fasali tare da zamanantar da ciniki a Arewacin Najeriya. Waiwaye: Muhimman Abubuwa A Dambarwar Abduljabbar Yau saura kwana 47 cif a daina […]
Kamfanin Galaxy Backbone (GBB) mallakin Gwamnatin Tarayya ya ce yana son yin amfanin da hanyoyin fasahar sadarwa na zamani a kasuwannin Jihar Kano.
Kamfanin ya ce zai yi hakan ne da nufin sauya fasali tare da zamanantar da ciniki a Arewacin Najeriya.
- Waiwaye: Muhimman Abubuwa A Dambarwar Abduljabbar
- Yau saura kwana 47 cif a daina karbar tsoffin kudade
Shugaban kamfanin, Farfesa Muhammad Abubakar ne ya bayyana hakan a Kano ranar Laraba, yayin wani taron masu ruwa da tsaki da kwastomomi mai taken: “Hanyoyin sadarwa na zamani don bunkasa ci gaban tattalin arziki.”
Ya ce zamanin da ake ciki yanzu na masana’antu da tattalin arziki ya fi ta’allaka ne ga ilimi da kuma fasahar sadarwa, inda ya ce kamfanin ya kafa cibiyar fasahar zamani ne a Kano kara matso da fasahar kusa da mutane.
“Takamaimai, muna son ganin mun samar da hanyar da za ta saukaka harkokin saye da sayarwa, ta yadda muka samar da wannan cibiya da kuma kayan aikin da za su sa bunkasa cinikayya a Kano, kasancewar Jihar cibiyar kasuwancin.
“Yanzu a duk fadin duniya, kamfanonin fasahar sadarwa ne suke tafiyar da ita, a yadda suke zama masu shiga tsakanin mai saye da mai sayar da kaya, wanda hakan ya cire ’yan ka-yi-na-yi daga kasuwanci, wadanda a baya suke sa farashin kaya ya tsauwala.
“Wannan ita ce alkiblar da kasuwanci yanzu yake fuskanta a duniya, kuma abin da kamfaninmu yake hankoron kawo wa Kano ke nan a matsayinta Na cibiyar kasuwanci,” inji Farfesa Muhammad.
Shugaban ya ce suna sa ran nan da karshen watan Disambar nan, kamfanin zai samar da ayyuka a jihohin Najeriya akalla 23, kuma suna fatan nan watannin shidan karshen 2023, za su karade ilahirin kasar.
Ita kuwa Gwamnatin Jihar Kano, wacce Kwamishinanta na Kimiyya da Fasaha, Idris Garba ya wakilta a wajen taron, ta yi alkawarin hada karfi da karfe da kamfanin don ganin hakarsa ta kai ga cim ma ruwa, inda ya ce gwamnatin ta kashe sama da Naira biliyan daya da rabi wajen samar da kayayyakin da za su bunkasa fasahar sadarwa a kwaryar birnin Kano.