Za mu sauya fasalin Kasuwar Gwari ta Duniya a Legas – Alhaji Usman Saffan

Shugaban Kasuwar Gwari ta Duniya da ke Mil 12 a Legas, Alhaji Usman Shehu Samffan wanda yake cika kwana 100  a matsayin shugaban kasuwar a yau Juma’a, ya bayyana wa Aminiya cewa bayyana cewa babban abin da ya sanya a gaba shi ne sauya fasalin kasuwar daga tsohon tsarinta zuwa sabo ta yadda za ta […]

Za mu sauya fasalin Kasuwar Gwari ta Duniya a Legas – Alhaji Usman Saffan

Alhaji Usman Shehu Saffan

Shugaban Kasuwar Gwari ta Duniya da ke Mil 12 a Legas, Alhaji Usman Shehu Samffan wanda yake cika kwana 100  a matsayin shugaban kasuwar a yau Juma’a, ya bayyana wa Aminiya cewa bayyana cewa babban abin da ya sanya a gaba shi ne sauya fasalin kasuwar daga tsohon tsarinta zuwa sabo ta yadda za ta yi gogayya da sauran kasuwannin kayan gwari da ke qasashen duniya da suka ci gaba.

Alhaji Usman Saffan ya ce, lokacin da ya karbi jan ragamar kasuwar daga tsohon shugabanta Alhaji Haruna Muhammad, ya yi alqawarin dorawa a kan kyawawan ayyukan da ya gudanar a kasuwar a tsawon shekarun da ya yi yana jagorantarta. “Da tsohon shugaban wannan kasuwa Alhaji Haruna Muhammad nake koyi, na yi aiki a qarqashin jagorancinsa na san irin aikace-aikacen ci gaban da ya yi domin bunqasa  kasuwar, zuwa yanzu cikin kwana 100 da muka yi muna jagorancin wannan kasuwa mun sauya mata fasali ta yadda za ta yi daidai da zamani. Mun qara tsayin katangarta mun tsabtace ta, mun yi maganin cinkoso ababen hawa a daura da ita, kuma mun yi aikin buda hanyoyin da suke shiga kasuwar domin kyautata shiga da ficen jama’a da ke hada-hada a kasuwar,” inji shi.

Alhaji Usman Saffan, ya ce shirye-shirye sun yi nisa wajen kafa cibiyar sadarwa ta zamani a kasuwar, inda ya ce yanzu zamani ya sauya ta yadda harkokin kasuwanci suka koma ta Intanet, don haka hukumomin kasuwar suna shirin samar da cibiyar kasuwanci ta hanyar sadarwar zamani a kasuwar domin bai wa ’yan kasuwar damar yin huldar kasuwanci kai-tsaye da takwarorinsu na duniya. “Yanzu harkar sadarwar zamani na  taka muhimmiyar rawa a sha’anin kasuwanci a duniya, don haka  ba za mu bari a bar mu a baya ba a wannan fanni.  Za mu yi iya qoqarin ganin mun tafi a zamanance, yanzu haka mun cimma nasara a ayyukan da muka faro wato tsabtar muhalli, kyautata tsaro da zaman lafiya, qulla kyakyawar alaqa da ’yan kasuwa da abokan kasuwancinmu da kuma gwamnatin Jihar Legas. Dama abin da gwamnatin ke buqata ke nan, a kyautata muhalli a tsabtace kasuwa sannan a zauna lafiya, muna iya qoqarinmu don tabbatar da wannan,” inji shi.

Aminiya ta zanta da fatake da dama da ke hada-hadar kasuwanci a kasuwar inda suka yaba kan  sauyin da suka gani a cikin qanqanen lokaci a kasuwar inda suka yi fatar ci gaba da bai wa shugabannin kasuwar goyon baya domin ciyar da ita gaba.