Za mu tabbatar da ‘A Kasa A Tsare’ a zabe – Buhari

A farkon makon nan ne wakilanmu suka zanta da dan takarar shugaban kasa a karkashin iunuwar jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari inda ya yi bayani a kan al’amurra daban-daban da suka shafi kasa da kuma zabe mai zuwa. Ga yadda hirar ta kasance: Wannan shi ne karo na hudu da kake takarar shugabancin Najeriya. Ko […]

Za mu tabbatar da ‘A Kasa A Tsare’ a zabe – Buhari

 Janar Muhammadu Buhari A farkon makon nan ne wakilanmu suka zanta da dan takarar shugaban kasa a karkashin iunuwar jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari inda ya yi bayani a kan al’amurra daban-daban da suka shafi kasa da kuma zabe mai zuwa. Ga yadda hirar ta kasance:

Wannan shi ne karo na hudu da kake takarar shugabancin Najeriya. Ko akwai wani abu da ka gani kuma kake tsammanin a wannan karon labarin zai bambanta da na baya?
kwarai kuwa, abu na farko shi ne kawancen jam’iyyun da suka hade wuri daya. Tun 2005, mun lura da cewa babu wata jam’iyyar adawa da za ta iya karawa da PDP kuma ta samu galaba, kuma mun lura cewa PDP ba ta da niyyar gudanar da mulkin adalci, kamar yadda muka gani shekaru 16 da take rike da mulki. Misali, idan ka duba tattalin arzikin kasarmu, a da can muna da kamfanin safarar jiragen sama (Nigerian Airways) da na jiragen kasa (Nigerian Railways) da na jiragen ruwa (Nigerian Shipping Line). Yanzu duk ina wadannan suke? Ka dubi kudin da ake ta kashe wa NEPA. Mu duba binciken da Majalisun Tarayya suka gudanar game da NEPA da maganar kudin fansho da na kamfanin man fetur. Sun gudanar da taron tattara bayanai a Abuja sannan kuma suka ziyarci sassa shida na kasar nan, suka tattara rahotonsu, suka aika wa bangaren zartarwa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar. Amma babu inda ka taba jin cewa an hukunta wadanda suka sace dukiyar al’umma a kasar nan.
Abu na biyu, duk da cewa tsarin aiki bai amince da haka ba, sai ga shi sojojin Najeriya da ma’aikatansu suna tattaunawa da kafafen watsa labarai na waje, suna fadin cewa ana tura su fagen daga ba tare ingantattun makamai ba. Haka kuma Majalisar Tarayya ta yi yunkurin biciken bin bahasin abin da ake kasafta wa sojoji da Ma’aikatar Tsaro na tsawon shekaru uku zuwa hudu – makudan kudi ne da suka kai tiriliyan da yawa. Kuma sun bukaci su kira shugabannin hukumomin tsaro, domin su je su bayyana musu abin da ke faruwa ga kudaden da ake ware wa tsaro, wadanda ake aikawa ga Ma’aikatar Tsaro domin sayen ingantattun kayan fada na zamani da na horarwa, amma dai irin wannan bincike an dakile shi, an lalata aniyarsa.
Misali, a jam’iyyar ANPP a 2003, lokacin da aka ce mun fadi zabe, mun kwashe watanni 30 a Kotun daukaka kara har zuwa Kotun koli. A 2007, mun kwashe watanni 18. A 2011, ina tsammanin mun kwashe watanni takwas zuwa tara, inda duk muke karewa a Kotun koli. Don haka duk wanda ke son ya san hakikanin abin da ya faru game da kokarin da muka yi, sai ya nemi bayanin shari’o’in da aka yi a Kotun koli, domin kuwa a yanzu sun zama kayan al’umma. Idan za ku tuna, a 2007, an raba Kotun koli zuwa gida biyu ne. Alkalai uku suka ce zaben gurbatacce ne, ba a gudanar da shi kamar yadda doka ta tanada ba, sauran alkalai uku kuma suka ce, duk da cewa akwai tangarda ga zaben amma duk da haka dai PDP ce ta yi nasara. Don haka sai Babban Joji ya mara wa ukun nan baya, dalili ke nan hudu suka rinjayi uku.
Yau kusan tsawon sama da shekara goma ke nan kake gogayya cikin siyasa, kana ta murzawa ba tare da gajiyawa ba. Wasu mutane na ganin cewa ya kamata ka huta domin matasa su samu kafar turzawa su ma…
Ba na son in mayar da takarar nan ta shugabancin kasa kayan gado. Idan da za ka tuno, na jure kan wannan buri saboda wasu mutane da suka rike ni a cikinsa. A 2010, lokacin da na fadi cewa daga wannan ba zan kara shiga ba. Amma sai magoya bayana da ke fadin kasar nan suka ce tun da dai ba cewa na yi na yi ritaya daga siyasa ba gaba daya, to bai kamata in bijire wa bukatunsu ba. Dalili ke nan ya sa masoyana suka hadu suka ce lallai tilas sai na sake tsayawa takara tun da dai jam’iyya ba ta yada ni ba. Abin da ya faru a zaben fidda gwani na bana, ya isa misali. Da masoyana ba su so in sake yin takara da ba su sake zabe na ba. Amma dai ka ga sakamakon zaben yadda ya nuna, kuma zabe ne aka yi na gaskiya da adalci. Don haka, tun da dai ban yi ritaya daga siyasa ba, ina ganin ina da rawar da zan taka, wajen ganin cewa an mulki kasar nan cikin adalci da gaskiya.
Gwamnatin da ke ci a yanzu tana shan suka har ma daga kasashen duniya, suna cewa ta gaza. Kana ganin wannan gazawar za ta taimaka maka ka samu nasarar lashe zaben nan cikin sauki?
Idan ka duba, gwamnatin nan ta yi tabargaza da kura-kurai masu yawa da suka kamata a ce an sallame ta. Wani abu mai muhimmanci shi ne, mu tabbatar da cewa mun yi gangamin yaki neman zabe da fadakarwa ga dukkan mazabun kasar nan, ta yadda duk kuri’ar da aka kada ta zama ta yi tasiri. Muna da misalin zabubbukan jihohin Ekiti da Osun da aka gudanar baya-bayan nan kuma muna sane da cewa babu abin da PDP ta iya illa magudin zabe, ta tura ma’aikatan tsaro marasa gaskiya, wadanda suke kama shugabannin jam’iyyun adawa suna kullewa, su sake su bayan an kammala zabe. Haka kuma suke shirya mutane su sace akwatunan zabe, su yi dangwalen karya, kamar kuma yadda suke buga takardun zabe na bogi. Duk mun gabatar da irin wadannan shaidun a kotu, a zabubbukan da suka gudana a baya.
Ka sha gaya wa kafafen watsa labarai zargin cewa ana yi maka magudin zabe, wadanne matakai kake shirin dauka domin ganin ka kare kuri’un da za a kada maka?
Yanzu na gama fada maka batun Ekiti da Osun. Ku duba yadda APC a Ekiti da shugabanninta suka hada kan al’umma suka wayar musu da kai a duk fadin jihar. Ba zan iya tuno yawan adadin shugabannin jam’iyyun adawa a mazabun jihar Osun da aka kame kuma aka sakaya su a wakafi ba. Wasu ma har gidajensu aka je, aka karya kofofinsu, aka kame su.
Shin me ya sanya wasu ’yan Najeriya suka kasa fahimtarka?
Ba na zaton cewa ba a fahimce ni ba kwata-kwata. Wadanda ba su fahimce ni ba da gangan ne kuma su ne ’yan kanzagin PDP da ake biyan su su yi haka. Abin da kawai zan ce ke nan.
Mene ne kudurinka a rayuwa?
Gaskiya da adalci a dukkan al’amuran rayuwa – tun daga shugabanci a gidanka zuwa duk wani mukami da za ka rike, ka tabbatar ka tafiyar da shi bisa gaskiya da adalci.
Kwanan nan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta gudanar da taron tuntuba da manema labarai. daya daga cikin sharuddan da ta gindaya shi ne, ba za a yarda kafafen watsa labarai su fadi kowane irin sakamakon zabe ba sai ita kadai hukumar zaben za ta yi haka. Kamar yadda kake kiran jama’a su kasa su tsare, ko ka gamsu da wannan sharadi da hukumar zaben ta gindaya?
Cigaba a shafi na 3

Daga shafi na 2

Ban gamsu ba. Zan bukaci jam’iyyata ta aika isassun wakilai kuma idan ma ta kama su bukaci masu zabe su bijire wa haka, domin kuwa akwai gyaran da aka yi wa dokokin zabe, wanda ya ce za a bayyana sakamakon zabe a kowace rumfar zabe da kowace matattarar sakamako da kowace karamar hukuma da kuma kowace jiha, sannan kuma daga karshe a tattara shi a bayyana a hedikwatar Hukumar Zabe ta kasa.
Yanzu ne ka ce suna da ikon da za su taimaka wa wadanda ke kan mulki, ko kana tunanin abin nan da suka fada, za a bari su aiwatar da shi?
Za mu yi iyaka kokarinmu wajen ganin an tabbatar da shi cikin doka kuma za mu iya ganewa, idan har sun karya doka. A kowace rumfar zabe, akwai jami’an hukumar INEC. Shin wannan yana nuna ba su amince da jami’ansu da suka aika a dukkan rumfunan zaben da ke kasar nan ne ba? Idan har sun amince da su. Su bari su fadi sakamakon zabe a dukkan rumfunan da suka gudanar da aiki, su yi haka a kowace mazaba, a kowace karamar hukuma, a kowace jiha.
Idan muka dawo batun rashin tsaro, wane mataki za ka fara dauka idan kana son magance matsalar ta’addanci idan an zabe ka?
Abu na farko da zan yi shi ne, zan yi kokarin gano babbar matsalar hukumomin tsaro, wato yadda suke tattara bayanan sirri. Zan binciko ina matsalar ta ke? Me ya sanya muka iya gudanar da babban yakin basasa ba tare da mun ciwo bashin ko kwabo ba kuma muka yi nasara? Amma ga shi yaki da wasu tsirarun ’yan ta’adda da suke zaune a wani dan lungu na Najeriya, ga shi kuma Gwamnatin Tarayya ke jagorantar lamarin, tana neman Majalisar Tarayya ta amince a ciwo bashin Dala biliyan daya, don a yaki ’yan ta’adda?
Game da ’yan matan Chibok, ka yi bayani game da su a baya amma muna son ka yi mana bayani. Idan kai ne, wane mnataki za ka dauka a kan al’amarin?
Ina da yakinin kuna sane da cewa lokacin da aka sace matan na Chibok, ina jin sai da aka kwashe makonni uku, kafin Shugaban kasa ma ya amince da cewa lallai an sace su. Na yi amanna da cewa hanyoyin tattara bayanai na hukumomin tsaron kasar nan sun lalace, ta yadda wannan mummunan al’amari zai faru ba tare da Shugaban kasa ya sani ba har zuwa makonni uku. Wannan abin mamaki ne!
Akwai bayanan da aka yi ta yadawa, cewa wajen zaben wanda zai mara ma baya, Tinubu ne ya tilasta maka daukar wanda ka dauka. Ina gaskiyar wannan batu kuma ta yaya kuka cin ma daukar zabo shi?
Tinubu bai tilasta mani daukar kowa ba. Tsarin yadda aka tafiyar da zaben a fili yake karara. Idan jam’iyyarka ta zabe ka, kana da ikon zabe. Jam’iyya ta zabe ni a matsayin dan takarar shugabancin kasa. An yi la’akari da abubuwa da dama, wadanda suka hada da kokari da irin goyon bayan da mutum yake ba jam’iyya, halayya da dabi’ar mutumin da ka gabatar. Abin da kawai za ka yi shi ne ka bukaci sunayen mutane daga jam’iyya, su kuma za su bi hanyoyin tantancewa, ta inda za su yi la’akari da shiyyar da mutum ya fito daga shiyyoyi shida na kasar nan. Babu yadda za a yi ka ce za ka dauki Mataimakin Shugaban kasa daga Arewa, inda kuma Shugaban kasa ya fito. Tsarin siyasa ma bai amince da wannan ba, domin abin zai zama bambarakwai ne. Jam’iyya ta ba ni sunayen, ni kuma na zabi daya. Wannan ita ce hanyar da ake bi kuma mun bi diddigi. Hatta ita kanta PDP ta zarge ni da cewa na gaza, yadda na dauki kwanaki shida kafin in zabi wanda zai mara mani baya. Al’amarin namu ba na gaggawa ba ne, sai mun kalailaice, mun bi tsarin da aka tanadar.
Yaya dangantarku take da Tinubu, musamman ma bayan al’amuran siyasa da al’amuran jam’iyya? Yaya za ka misalta wannan mutumin a ganinka?
Shi mutum ne mai jajircewa, dan jam’iyya na hakika. Ina tunanin da ba domin shi da Cif Akande da kuma wadansu daga cikinmu ba, wannan  hada kan jam’iyyun da muka yi, da bai yiwu ba. Dole ne sai da mutane suka sadaukar da shugabancin da suke yi a wadansu jam’iyyu kafin mu tabbatar da ita. Wannan kuma shi ne abu mafi alfanu ga Najeriya. Tana  bukatar sadaukarwa mai yawa.
Wadansu na ganin cewa zaben Osinbanjo da ka yi ya zama bambarakwai. Tun yaushe ne ka hadu da shi, kuma me ya sanya ka zabe shi?
Mene ne abin bambarakwai a nan? Ba mu zabe shi daga cikin mutane ’yan karan-kada-miya ba. Wane ne ma mutumin da na zaba a matsayin mataimaki a can baya? Shi ma Fasto ne kuma Bayarabe. A 2003, Chuba Okadigbo na zaba, wanda dan Roman Katolika ne. A 2007, na zabi Ezuibike ne, wanda Ibo ne mai bin darikar Katolika.