Za mu tabbatar da tsaron masu yi wa kasa hidima a Yobe — Buni

Mun dauki kwararan matakai na tabbatar da tsaron lafiyar masu yi wa kasa hidima a Jihar Yobe.

Za mu tabbatar da tsaron masu yi wa kasa hidima a Yobe — Buni

Mai Mala Buni

Gwamna Mai Mala Buni ya ba da tabbacin tsaron dukkanin matasa masu yi wa kasa hidima (NYSC) da aka tura Jihar Yobe. 

Gwamnan ya sanar da hakan ne a yayin bikin rantsar da sabbin matasa masu yi wa kasa hidima rukunin ‘B’ stream I na shekarar 2023 a sansanin horar da su da ke Dazigau.

Aminiya ta ruwaito cewa Gwamna Buni ya samu wakilcin babban mai taimaka masa na musamman kan samar da arziki da ayyukan yi, Abdullahi Bego.

A cewarsa, gwamnatin jihar ta dauki kwararan matakai na tabbatar da tsaron lafiyar matasan a Jihar Yobe.

A nata bangaren, Ko’odinetan NYSC ta Jihar Yobe, Misis Hafsat Yerima, ta yi maraba da matasan da aka turo Yobe hidimta wa Najeriya.

“Dole ne mu gode wa Allah Madaukakin Sarki da Ya yi muku jagora baki daya zuwa sansanin horarwa a nan Yobe.

“A madadin Darakta Janar na hukumar, ma’aikata da daukacin jami’an hukumar da ke aiki a Jihar Yobe, ina so in taya ku murnar kammala karatun ku na manyan makarantu daban-daban wanda ya ba ku damar shiga cikin gurbin wadanda za su yi wa kasa hidima.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta