Za mu tabbatar da zaman lafiya ko ta halin kaka – Janar Buratai

Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya Laftana Janar Yusuf Tukur Buratai ya nanata cewa sojojin Najeriya suna aiki ba dare ba rana don tabbatar da samuwar zaman lafiya ko ta halin kaka a kasar nan. Laftana Janar Buratai ya bayyana haka ne yayin wata ziyara da ya kai wa Gbong Gwom na Jos, Da Jacob Gyang Buba […]

Za mu tabbatar da zaman lafiya ko ta halin kaka – Janar Buratai
Za mu tabbatar da zaman lafiya ko ta halin kaka – Janar Buratai

Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya Laftana Janar Yusuf Tukur Buratai ya nanata cewa sojojin Najeriya suna aiki ba dare ba rana don tabbatar da samuwar zaman lafiya ko ta halin kaka a kasar nan. Laftana Janar Buratai ya bayyana haka ne yayin wata ziyara da ya kai wa Gbong Gwom na Jos, Da Jacob Gyang Buba a fadarsa da ke Jos a ranar Litinin da ta gabata.
Janar Buratai wanda yake ziyarar kananan rundunonin da ke karkashin Rundunar Sojojin Najeriya ta 3 ya bayyana cewa sun karya lagon mayakan Boko Haram hade da toshe duk wata kafa da za ta ba su damar kara haduwa a wuri daya a duk sassan Najeriya.
Ya ce fadi-tashi da jajircewar da sojoji suka yi wajen yakar Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas ya taimaka sosai wajen dakile tashe-tashen bama-bamai a tasoshin motoci da wuraren ibada a Najeriya.
Ya tabbatar da cewa sojoji za su ba al’ummar Jihar Filato kariya ta musamman, sannan ya nanata cewa ’yan Najeriya ba za su kara ganin miyagun hare-hare daga mayakan Boko Haram kamar yadda suka gani a baya ba.
Ya yaba wa Gbong Gwom na Jos bisa ga gudunmawa da hadin kan da ya ba sojoji, inda hakan ya taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu cikin karfin gwiwa.
Ya jajanta wa Gbong Gwom na Jos sakamakon kashe Saf Ron Kulere na karamar Hukumar Bokkos Mista La’azarus Agai da wadansu ’yan bindiga suka yi a kwanakin baya.
A lokacin da yake jawabin maraba, Gbong Gwom na Jos, Da Jacob Gyang Buba ya roki sojoji da sauran jami’an tsaro su kara zage damtse wajen gano wadanda suka kashe Saf Ron Kulere, sannan a tabbatar an hukunta su daidai da abin da suka aikata. Ya yaba wa sojojin kan sadaukarwar da suka yi wajen ganin an tabbatar da zaman lafiya da doka da oda ba wai kawai a Jihar Filato ba, har da daukacin Najeriya. Ya kuma gode wa Shugaba Muhammadu Buhari bisa ga yadda ya jajirce wajen yaki da ta’addancin a Najeriya.