Za mu tafi da kowa a Jos ta Arewa – Mai Madara
Sabon Sakataren karamar hukumar Jos ta Arewa dake Jihar Filato, Alhaji Hassan Isah Mai Madara ya bayyana cewa sababbin shugabannin riko na karamar hukumar Jos ta Arewa da aka zaba, zasu tafi da kowa da kowa a karamar hukumar ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba. Alhaji Hassan Mai Madara ya bayyana haka […]

Sabon Sakataren karamar hukumar Jos ta Arewa dake Jihar Filato, Alhaji Hassan Isah Mai Madara ya bayyana cewa sababbin shugabannin riko na karamar hukumar Jos ta Arewa da aka zaba, zasu tafi da kowa da kowa a karamar hukumar ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba. Alhaji Hassan Mai Madara ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya a garin Jos.
Ya ce zamu yi iyakar kokarinmu wajen ganin cewa wannan karamar hukuma ta ci gaba da zaman lafiyar da aka samu. Ta hanyar hada kan al’ummar wannan karamar hukuma tare da tafiya da kowa ba tare da nuna wariyar addini ko kabila ba.
Ya ce zamu yi haka ne domin tallafawa kudurin gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong na ganin an ci gaba da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Filato.
“Babu shakka idan aka ci gaba da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali zamu sami nasarar aiwatar da abubuwan ci gaba a wannan karamar hukuma ta Jos ta arewa. Sannan al’umma su bamu goyan baya da hadin kai, tare shawarwarin da zamu taimaka masu wajen gudanar da abubuwan ci gaba a wannan karamar hukuma.”