Za mu taimaka wa Buhari ta fuskar samar da tsaro – Sarkin Keffi(5)
Mai martaba Sarkin Keffi a Jihar Nasarawa, Dokta Shehu Usman Yamusa na Uku, ya ce sarakunan kasar nan za su ci gaba da ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin jihohi goyon baya kan matakan da suke dauka wajen magance matsalar tsaro da kawo zaman lafiya a kasar nan.Sarki Shehu Yamusa ya bayyana haka ne […]
Mai martaba Sarkin Keffi a Jihar Nasarawa, Dokta Shehu Usman Yamusa na Uku, ya ce sarakunan kasar nan za su ci gaba da ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin jihohi goyon baya kan matakan da suke dauka wajen magance matsalar tsaro da kawo zaman lafiya a kasar nan.
Sarki Shehu Yamusa ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a masaukin Shugaban kasa da ke Birnin Kebbi a lokacin da ya kai ziyara ga Mai martaba Sarkin Gwandu Dokta Muhammadu Iliyasu Bashar.
Sarkin ya ce, dalilin ziyararsa Jihar Kebbi, shi ne domin tattaunawa da Mai martaba Sarkin Gwandu kan yadda sarakuna za su ci gaba da ba da tasu gudummawa domin kawo karshen ta’addanci da satar shanu da garkuwa da mutane da ake yi a Arewa.
Sarkin ya ce, sarakuna da hakimai da dagatai da masu ungwanninsu, a shirye suke a koyaushe su wayar wa jama’arsu kai a kan bakon ido da ba su yarda da shi ba, su kai rahoto wurin da ya dace. Kuma jama’a da ake ba gidaje haya dole ne su san inda mutum ya fito ko inda yake aiki ko sana’arsa kuma a san inda wanda ya kawo shi ko wanda ya ba shi gidan hayar, domin ta irin haka ne za a iya gane miyagun da suke mutane.
Sarkin ya ce “Tunda yanzu an samu Shugaban kasa mai yi da gaske don kawar da ta’addanci a kasar nan, dole mu ma shugabannin al’umma da su kansu al’ummar mu taimaka wa Shugaban kasa da gwamnoni mu tona duk wani mai ta’addanci ko barayin shanu.”
Sarkin ya yi kira ga al’ummar Arewa su dauki dukkan matakan da suka kamata domin habaka noma da kiwo da kuma abin da ya shafi ma’adanai ganin yadda darajar man fetur take kara faduwa. Ya bukaci kuma mutane su rika bin doka a oda da kuma kaffa-kaffa da dukiyar al’umma su rungumi harkar ilimi da zaman lafiya.