Za mu taimaka wa gwamnatin Nijar yakar dakarun ECOWAS —Mali, Burkina Faso

Sun kuma yi barazanar ficewa daga ECOWAS din gaba daya

Za mu taimaka wa gwamnatin Nijar yakar dakarun ECOWAS —Mali, Burkina Faso

Abdourahmane Tchiani

Kasashen Mali da Burkina Faso sun yi barazanar ficewa daga Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma (ECOWAS) domin su tamaka wa gwamnatin mulkin soji ta kasar Nijar daga mamayar dakarun kungiyar.

Kasashen biyu, wadanda a ’yan shekarun nan sojoji suka kwace shugabancinsu, a cikin wata sanarwa a ranar Talata, sun ce suna goyon bayan juyin mulkin na Nijar, kua za su taimaka mata ta yaki yunkurin mamaye kasar daga ECOWAS.

Mali da Burkina Faso sun yi gargadin cewa, “Duk wani yunkuri na mamaye Jamhuriyar Nijar wani mataki ne na ayyana yaki a kan kasashenmu na Mali da Burkina Faso,” in ji sanawarar.

Sun kuma ce matukar ECOWAS ta mamaye Nijar, to babu makawa za su fice daga kungiyar sannan su taimaka mata wajen kare ’yan kasarta daga mamayar da za a yi musu.

Kasashen sun kuma soki lamirin kungiyar ta ECOWAS, inda suka zarge ta da nuna munafunci.

Sanarwar dai ta biyo bayan matakin ECOWAS na karshen mako inda ta ba sojojin mako daya su dawo da tsohon Shugaban Kasar, Mohammed Bazoum sannan su koma barikokinsu.

Kungiyar ta kuma yi barazanar katse dukkan wata harkar kasuwanci da kuma kulle asusun ajiyarta na bankuna da kuma sararain samaniyarta.

A ranar Larabar da ta gabata ce dai sojojin Nijar suka yi wa Bazoum juyin mulki sannan suka ayyana dokar ta baci da kuma kulle dukkan iyakokin kasar na sama da na ruwa.

Janar Amadou Abdramane, dai shi ne ya ayyana kansa a matsayin sabon Shugaban Kasar na soja.

(AFP)