Za mu taimaka wa Najeriya ta gyara matatun manta – Saudiyya

Gwamnatin kasar Saudiyya ta yi alkawarin zuba jari domin farfaɗo da matatun man Najeriya da kuma taimaka wa gwamnati ta aiwatar da tsare-tsaren daidaita darajar Naira. Yariman Saudiyya, Muhammad Bin Salman ne ya yi alkawarin yayin tattauna da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a gefen taron kasar da kasashen Afirka da yake gudana a Riyadh, babban […]

Za mu taimaka wa Najeriya ta gyara matatun manta – Saudiyya

Yarima mai jiran gadon Masarautar Saudiyya, Muhammad Bin Salman

Gwamnatin kasar Saudiyya ta yi alkawarin zuba jari domin farfaɗo da matatun man Najeriya da kuma taimaka wa gwamnati ta aiwatar da tsare-tsaren daidaita darajar Naira.

Yariman Saudiyya, Muhammad Bin Salman ne ya yi alkawarin yayin tattauna da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a gefen taron kasar da kasashen Afirka da yake gudana a Riyadh, babban birnin kasar.

Saudiyya ta kuma yi alkawarin tallafa wa Najeriya, ta hannun Babban Bankin Najeriya (CBN), domin a farfaɗo da darajar Naira.

Yarima Muhammad, a cikin wata sanarwa da Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya kuma yabawa manufofin tattalin arzikin da Shugaba Tinubu yake aiwatarwa.

A cewar Yariman na Saudiyya, ƙasar shi ta ƙagu ta ga Najeriya tana bunkasa a karkashin Shugaba Tinubu, musamman a matsayinta na jagaba a Afirka.