Za mu taimaka wa Shugaba Buhari – Abdullahi Garba

dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Mariga da Mashegu da Kwantagora da Wushishi Honarabul Abdullahi Idris Garba ya ce za su taimaka wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen aiwatar da manufofin kasafin kudin da ya rattaba wa hannu a kwanakin baya.Honarabul Abdullahi Idris Garba ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da wakilin Aminiya […]

Za mu taimaka wa Shugaba Buhari – Abdullahi Garba
Za mu taimaka wa Shugaba Buhari – Abdullahi Garba

dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Mariga da Mashegu da Kwantagora da Wushishi Honarabul Abdullahi Idris Garba ya ce za su taimaka wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen aiwatar da manufofin kasafin kudin da ya rattaba wa hannu a kwanakin baya.
Honarabul Abdullahi Idris Garba ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da wakilin Aminiya a Kwantagora a karshen makon jiya, inda ya ce wannan ne karo na farko da Shugaban kasa mai ci ya gabatar da kasafin kudin da baki dayan ’yan Majalisar Tarayya suka amince da shi saboda an tsara shi ne yadda zai yi tasiri kai-tsaye a kan talakawa. “Saboda haka za mu ba da gudunmawarmu don ganin Shugaban kasa ya samu nasarar manufofin kasafin kudin,” inji shi.
dan Majalisar ya ce babban sirrin da ya sa baki dayan ’yan majalisar suka dauki matakin shi ne sun san cewa Shugaba Muhammadu Buhari mutum ne mai fada da cikawa.
Da ya juya kan yadda za a sarrafa kudin da Hukumar EFCC ta kwato daga hannun wadanda suka sace kudin Najeriya, dan majalisar ya ce doka ta tanadi yadda za a yi da kudin.
Ya ce su a matsayinsu na ’yan majalisa sun tabbata cewa Shugaban kasa zai bi hanyoyin da doka ta tanada domin ya sarrafa su yadda talaka zai san ana mulki na gaskiya a kasar nan.
Dangane da shirin da ya gabatar na tallafa wa mata da matasa fiye da 650, Honarabul Abdullahi Garba, ya ce mutanen mazabarsa ne suka yi sanadin kasancewarsa a majalisar wakilai kuma ya san halin da suke ciki. Ya ce don haka ya tattauna da masu ruwa-da-tsaki a kan babban abin da ya kamata ya yi don taimaka musu domin su samu saukin rayuwa.
Da yake karin haske, daraktan gudanar da shirin, Barista Lawal Yusuf, ya ce dan majalisar ya raba babura 120 da kekunan dinki 120 ga al’ummarsa. “Haka nan ya raba famfunan ban-ruwa da keke Napep guda 30, sai mata 50 da suka samu tallafin Naira dubu asihirin-ashirin kuma ya raba bas-bas hudu ga kungiyoyin addini da ke mazabar dan majalisar,” inji shi.
Wasu daga cikin wadanda suka samu tallafin sun yaba da matakin da dan majalisar ya dauka na taimakon marasa karfi daga lokaci zuwa lokaci.