Za mu tallafa wa Ukraine da jiragen yaki —Birtaniya

Birtaniya za ta horar da jami’an sojin Ukraine yadda za su yi amfani da sabbin makamai.

Za mu tallafa wa Ukraine da jiragen yaki —Birtaniya

Ma’aikatar Tsaron Birtaniya da ke birnin Landan.

Birtaniya za ta ba wa Ukraine tallafin jiragen ruwa maras matuka da ka iya lalubo muggan nakiyoyin da Rasha ta binne a gabar teku, in ji ma’aikatar tsaron kasar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da da Sakataren Tsaron Birtaniya, Ben Wallace ya fitar a ranar Asabar.

Sanarwar ta ce jiragen na iya nutso mai cin dogon zango har mita 100 a kasa, kana kuma ana iya amfani da su a wuraren da ke sa sassaucin zurfi na ruwan teku a cikin hanzari.

Ko baya ga kyautar jiragen guda shida, DW ya kuma ruwaito Ma’aikatar Tsaron ta Birtaniya tana shan alwashin horar da jami’an sojin Ukraine yadda za su yi amfani da sabbin makamai a wani mataki na kare kansu daga mamayar Rasha.

Ana dai zargin ko akwai yiwuwar Rasha ta binne manyan nakiyoyi a karkashin tekun Ukraine don haddasa tarnaki wa gabar ruwa Bahar Aswad da Ukraine ke amfani da ita wajen fitar da kayayyakin abinci da take nomawa zuwa kasuwannin duniya.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos