‘Za mu tallafa wajen inganta koyarwa a makarantun firamaren Katsina’

Sababbin malaman makarantun firamare da gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da su bayan tantancewa sun sha alwashin inganta koyarwa a makarantun jihar domin nuna farin cikinsu a kan yadda gwamnatin jihar ta kula da su da kuma yunkurinta na sake farfado da ilimi tun daga tushe. A zantawarsa da Aminiya a Katsina, mai magana da […]

‘Za mu tallafa wajen inganta koyarwa a makarantun firamaren Katsina’
‘Za mu tallafa wajen inganta koyarwa a makarantun firamaren Katsina’

Sababbin malaman makarantun firamare da gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da su bayan tantancewa sun sha alwashin inganta koyarwa a makarantun jihar domin nuna farin cikinsu a kan yadda gwamnatin jihar ta kula da su da kuma yunkurinta na sake farfado da ilimi tun daga tushe.
A zantawarsa da Aminiya a Katsina, mai magana da yawun malaman da tsohuwar gwamnatin jihar ta dauka aiki bayan an yi zabe, Malam Mohammad Abubakar Masanawa ya ce, “Bayan godiya ga wannan gwamnati a kan biyanmu dukkan hakkokinmu, wato albashi na tsawon wata takwas, tare da ariyas da duk muke bi bayan ta saurari kokenmu kuma ta tantance. Wannan abin ya ba mu matukar mamaki, an kuma bari mu ci gaba da aikinmu a matsayin malamai.”
Malam Mohammad ya ce matakin da gwamantin Masari ta dauka bullo da shi ya dace, “A da mu 732 ne waccan gwamnatin ta dauka aikin koyarwar amma daga cikinmu mutum 460 ne ke da takardar shaidar malanta, wasu sakandare ce suka gama aka dauke su. Amma wannan tantancewa da gwamnati ta fitar da masu takardun koyarwar ne kawai ta dauka ya yi daidai, su ma wadanda aka sallamar bayan an biya su sun gane cewa lallai an yi musu adalci kuma sun gamsu da wannan mataki,” inji shi.
Malamin ya ce, a yanzu baya ga zage damtse su biya bashin da ake bin su, babu wani abin da za su yi.
Malam Abubakar Nasir ’Yar’aduwa daya daga cikin malaman, cewa ya yi, bai ga dalilin nuna adawa da gwamnatin Katsina kakkashin Gwamna Masari da wasu ke yi ba musamman kan batun da ya shafi ilimi. “Farko ina cikin masu ganin laifin wannan gwamnati duk kuwa da cewa ba ita ce ta dauke ni aiki ba, amma ganin ta biya ni dukkan hakkokina ciki har da wadanda ya kamata a ce tsohuwar gwamnatin ce ta biya, wannan ya sanya ni canja tunani, kuma tabbas zan yi iya kokarina in ga na sauke nauyin da ya rataya a wuyana ta fuskar koyarwa.”