‘Za mu tallata katin nema wa Buhari kudi a kowane yankin Najeriya’

kungiyar Magoya Bayan Janar Muhammadu Buhari ta yi alwashin tallata katin neman kudi ga dan takarar Shugaban kasar a karkashin Jam’iyyar APC, a kowane sako na Najeriya ta hanyar amfani da ofishoshinta da ke kowane sashi na kasar nan.  Shugaban kungiyar ta kasa Alhaji Umar Faruk Muhammad ne ya bayyana haka a yayin zantawa da […]

‘Za mu tallata katin nema wa Buhari kudi a kowane yankin Najeriya’
‘Za mu tallata katin nema wa Buhari kudi a kowane yankin Najeriya’

kungiyar Magoya Bayan Janar Muhammadu Buhari ta yi alwashin tallata katin neman kudi ga dan takarar Shugaban kasar a karkashin Jam’iyyar APC, a kowane sako na Najeriya ta hanyar amfani da ofishoshinta da ke kowane sashi na kasar nan. 

Shugaban kungiyar ta kasa Alhaji Umar Faruk Muhammad ne ya bayyana haka a yayin zantawa da wakilinmu a Abuja, inda ya bayyana farin cikinsa a kan yadda katin neman kudin ke kara samun karbuwa wajen jama’a daga yankunan kasar nan daban-daban. Ya ce kungiyarsu ta tura daya daga cikin jagororinta zuwa babban ofishin Janar Buhari Organization da ke Abuja, don tattaunawa a kan al’amarin. Ya yaba kan yadda jama’a ke rungumar kungiyar wadda ya ce ke da rassa a duk yankunan Najeriya.
Ya ce ayyukan kungiyar tasu sun hada da fadakar da al’umma muhimmancin yin zabe da jajiircewa wajen ganin an mallaki katin zabe, sai kuma kada wa Buhari kuri’a idan lokacin zabe ya zo. Ya ce suna hulda da jama’ar ne ta matakin kungiya, inda suke zantawa da kungiyoyi tare da bayyana musu niyyarsu, kuma ya ce suna samun gagarumar karbuwa.

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato

Kotu ta soke hukuncin yi wa Jam’iyyar NDC rijista