Za mu tattauna da Boko Haram idan…

A ziyarar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai Amurka ya amsa tambayoyin fitacciyar ’yar jaridar nan ta gidan talabijin na CNN da ke Amurka Misis Christiane Amanpour inda ya bayyana fatarsa ga kawo karshen matsalolin da suka dabaibaye Najeriya: Shugaban kasa ka bukaci Amurka ta taimaka maka wajen yaki da Boko Haram. Mene ne […]

Za mu tattauna da Boko Haram idan…

A ziyarar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai Amurka ya amsa tambayoyin fitacciyar ’yar jaridar nan ta gidan talabijin na CNN da ke Amurka Misis Christiane Amanpour inda ya bayyana fatarsa ga kawo karshen matsalolin da suka dabaibaye Najeriya:

Shugaban kasa ka bukaci Amurka ta taimaka maka wajen yaki da Boko Haram. Mene ne ainihin abin da ka nema kuma wace amsa ka samu daga Shugaba Obama?
Amurka tana jagorantar kasashe Bakwai masu karfin arziki (G7) kan alkawarin da suka yin a tallafa wa Najeriya. Don haka mun kawo bukatunmu da suka hada da horarwa da samar da kayan aiki da samun bayanan sirri ga Najeriya ta yadda za ta iya yakar Boko Haram.
Ka ambaci tattalin arziki da faduwar farashin mai a watannin baya. Yaya za ka fuskanci wannan matsala. Domin hakan ne abin da mutanenka suke bukata?
Mutanena ina da yakinin abu na farko da suke bukata shi ne zaman lafiya a kasar ta dawo ta yadda rayuwa za ta koma daidai, a sashin Kudu na kasar masu dauke da makamai na ci gaba da kafar ungulu ga cibiyoyin man fetur da satar mutane don neman kudin fansa, sannan a Arewa maso Gabas Boko Haram na ci gaba da ta’addannci. Yanzu babban abin da ’yan Najeriya suka fi damuwa da shi, shi ne samu hanyar warware wadannan abubuwa. Babu abin da zai gudana har sai an samar da zaman lafiya a kasar.
Duk da alwashin da ka sha na magance Boko Haram, rahotanni daga kasarka na cewa akalla mutum 400 Boko Haram suka kashe tunda ka zama Shugaban kasa. Kuma rahoton kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Duniya (Amnesty International) ya ce sojojinka sun rasa martaba da amincewar jama’a saboda tsabagen tauye hakkin jama’a, sun kashe kimanin mutum dubu takwas. Yaya kake jin sojojin za su iya tunkarar Boko Haram, su kuma samu amincewar jama’a?
To, kwanan nan na fadi a taron Hukumar Tafkin Chadi, inda muka yi ittifakin kafa rundunar hadin gwiwa ta musamman, don haka abin da ya faru a baya kafin yanke wannan shawara za mu bari a binciki tuhumar keta hakkin dan Adam. Kuma da wannan ina da yakinin kun san shawarar da wannan gwamnati ta yanke – Gwamnatin Najeriya – na sauya shugabannin sojojin kasar.
Yaya batun ’yan matan Chibok su 200 ko fiye da aka sace dogon lokaci; kuma akwai bayanan da ke cewa Boko Haram da suka kama su, suna son a yi musayarsu da mambobinsu da ke tsare, shin gwamnatinka a shirye take ta yi musayar ’yan mata da wakilansu?
Wajibi ne mu yi taka-tsantsan kan hakikanin wadanda ke da’awar shugabancin Boko Haram, cewa za a iya sulhuntawa da su. Tilas mu yi taka-tsantsan sosai, kuma muna bi a hakali saboda muna son mu mayar da su ga iyayensu da kuma makarantarsu lafiya.
Ke nan ba ka amince ba, ko za ka duba yiwuwar tattaunawa da Boko Haram idan ka tantance hakikanin wadanda suka tunkare ka?
Ba zan ki ba, na gaya miki babbar manufarmu a matsayin gwamnati a kubutar da ’yan matan nan lafiya kalau su koma makarantarsu a kula da su, su dawo cikin hayyacinsu kamar kowa. Idan muka gamsu cewa shugabannin da suka gabatar da kansu za su iya dawo da ’yan matan nan lami lafiya, za mu amince a tattauna kan abin da suke bukata.
Ka zo gadon mulki a wani yanayi da ake ganin za ka fi Shugaban da ya gabata a bangaren tsaro da yaki da cin hanci da rashawa da inganta tattalin arziki da sauransu. Amma akwai daruruwan mutane da aka kashe bayan ka zama Shugaban kasa. Ta yaya za ka fiye da shi?
Ina jin za a iya kama ni kan alkawarin da na yi ne nan da shekara uku da kashi uku na shekara a gaba. Ina jin a mako 12 ko fiye, gaggawa ce ga kowane mutum ya yanke hukunci kan alkawurran da na yi lokacin kamfe.
Yaya batun alkawarnka na tuttuge cin hanci da rashawa, kuma idan ta bayyana wasu daga cikin wadanda aka kama ’yan jam’iyyarka ne ko abokanka; za ka iya hukunta su?
Wajibi ne in yi haka; babu batun dan wata jam’iyya ko wani mutu da doka za ta kasa aiki a kansa.
Ko ka ji ba dadi cewa Shugaba Obama ba zai je Najeriya ba, wadda ita ce mafi girma da karfin tattalin arziki a a Afirka?
Ba zan ce ban ji dadi ba, amma zan so ya sauya ra’ayinsa ya zo Najeriya.
Ka tambaye shi, kuma ya ce zai je?
Eh, na bukace shi, kuma zan aika masa da takardar gayyata.
Bari in tambaye ka kan wasu shugabannon Afirka da suka shude: kamar tsohon shugaban kama-karya nan a Chadi, Hissene Habre da ake yi masa shari’a – ko ake kokarin yi masa shari’a – a Senegal; shin ka goyi bayan yadda ake shari’a ga shugaban Afirka a Afirka, maimakon Kotun Duniya?
Shari’a shari’a ce ko a yi ta a Afirka ko wani wuri daban a duniya. Abu mai muhimmanci dai shi ne a yi adalci. Duk shaidar da masu gabatar da kara a Senegal suke da ita su yi kokari su nuna wa duniya kuma su yi masa shari’a kamar yadda dokokin duniya da na ’yancin dan Adam suka nuna.
Wato ka goyi bayan tsarin ke nan?
Na goyi bayan duk wata hanya da ta ginu kan adalci.