Za mu tona asirin duk limamin da ya karbi kudin Jonathan – Malam Ibrahim Jahun
Malam Ibrahim Hassan Jahun shi ne Sakataren Watsa Labarai na Majalisar Da’awa reshen Jihar Bauchi a tattaunawarsu da wakilinmu a ofishinsa da ke Bauchi ya yi fashin baki game da kudin da ake zargi ’yan siyasa musamman Gwamnatin Tarayya na raba wa malaman addinai a Najeriya: Aminiya: Farko za mu so ka gabatar da kanka?Malam […]
Malam Ibrahim Hassan Jahun shi ne Sakataren Watsa Labarai na Majalisar Da’awa reshen Jihar Bauchi a tattaunawarsu da wakilinmu a ofishinsa da ke Bauchi ya yi fashin baki game da kudin da ake zargi ’yan siyasa musamman Gwamnatin Tarayya na raba wa malaman addinai a Najeriya:
Aminiya: Farko za mu so ka gabatar da kanka?
Malam Ibrahim Hassan Jahun: Sunana Malam Ibrahim Hassan Jahun, babban sakataren watsa labarai na Majalisar Da’awa da ke shiga sako da lungu domin karantar da al’umma kan addinin Musulunci.
Aminiya: Me za ka ce game da makudan kudin da ake zargin ’yan siyasa (musamman gwamnati) na raba wa malaman addinai a Najeriya?
Malam Ibrahim Hassan Jahun: A gaskiya muna matukar bakin ciki bisa yadda wasu daga cikin malaman addinai suka zamo ba su da wani aiki sai karbar makudan kudi daga hannun ’yan siyasa musamman masu mulki da kuma masu neman mulki ido rufe. Kowa ya san cewa wadannan kudi da ake bayarwa ana son amfani da malaman ne domin an buga gangar siyasa a Najeriya, ba mu ji dadin yadda ake raba kudin ba.
Aminiya: A nan Jihar Bauchi ko akwai wadanda kuka samu labari sun karbi kudin?
Malam Ibrahim Hassan Jahun: Har zuwa wannan lokaci da muke tattaunawa babu wani malami da muka samu labari ya karbi kudin sai dai kuma akwai wata alama da muka gani na wasu daga cikin almajirai sun fara tallata wannan gwamnati ta kafofin watsa labarai da jaridu. Kowa ya san cewa da yawa daga cikin ’yan Najeriya sun gaji da wannan gwamnati wacce ta gagara samar da tsaro da kayayyakin more rayuwa ga al’umma. Za mu ci gaba da sa ido sosai game da wadannan malamai da almajirai domin yanzu kan mutane ya fara wayewa.
Aminiya: Shin laifi ne idan an ba malamai kudi a wannan lokaci na kamfe?
Malam Ibrahim Hassan Jahun: Duk malamin da yake kishin al’ummarsa bai dace ya karbi irin wadannan kudi ba, domin kowa ya san cewa ana so a yi amfani da shi ne domin tallata ’yan takara. Akwai lokutan da ake karbar kyauta daga wajen hukumomi akwai kuma wasu lokutan da ba a karbar kyauta da wajen masu mulki. Ina tabbatar maka cewa duk malamin da ya karbi kudin ’yan siyasa mutuncinsa yakan zube a idon al’umma. Idan malamai suka gurbace, to, tabbas makomar al’umma ba zai yi kyau ba, domin malamai su ne fitilar haskaka kowace al’umma a fadin duniya.
Aminiya: Mene ne sakonka ga limaman masallatan Juma’a na Jihar Bauchi?
Malam Ibrahim Hassan Jahun: Babban sakona ga limaman jJihar Bauchi shi ne ya kamata su ji tsoron Allah, su tuna cewa duk abin da mutum ya aikata zai ba da amsa ranar gobe kiyama, kuma duk limamin da muka ji yana cewa a zabi cancanta, to, tabbas ya karbi kudin ’yan siyasa, musamman gwamnati.
Aminiya: Su kuma malaman addinai mene ne sakoka gare su?
Malam Ibrahim Hassan Jahun: Babban sakona ga malaman addinai a Jihar Bauchi shi ne ya kamata kowa ya shafa wa kansa ruwa, wallahi duk malamin da muka samu ya karbi kudin Jonathan to za mu tona asirinsa ta kafofin watsa labarai na zamani. Bayan haka za mu bi masallata daya bayan daya domin fada wa al’umma cewa malam wane ya karbi kudi domin yin kamfe ga Shugaba Jonathan ko wani dan takara, tabbas ba za mu sassauta masa ba, duk inda muka je sai mun fallasa asirinsa ga al’umma.