Za mu tsige Yakubu Dogara idan… – Da’u Aliyu

dan Majalisar Tarayya daga Mazabar Buji da Birnin Kudu daga Jihar Jigawa, Injiniya Magaji Da’u Aliyu ya nuna damuwa kan keta haddin da Shugaban Majalisar Tarayya Barista Yakubu Dogara ke yi wa uwar Jam’iyyar APC da kuma Shugaban kasa Muhammadu Buhari.Injiniya Magaji Da’u ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai […]

Za mu tsige Yakubu Dogara idan… – Da’u Aliyu
Za mu tsige Yakubu Dogara idan… – Da’u Aliyu

dan Majalisar Tarayya daga Mazabar Buji da Birnin Kudu daga Jihar Jigawa, Injiniya Magaji Da’u Aliyu ya nuna damuwa kan keta haddin da Shugaban Majalisar Tarayya Barista Yakubu Dogara ke yi wa uwar Jam’iyyar APC da kuma Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Injiniya Magaji Da’u ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a babura bayan ya kai ziyarar girmamawa ga Gwamnan Jihar Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar a lokacin Sallar da ta gabata, inda ya ce ba za su amince a ci gaba da ci wa jam’iyyar mutunci ba alhali ita ce ta yi sanadin shigarsu majalisar.
Injiniya Magaji Da’u ya ce har yanzu akwai sauran rina a kaba tsakanin shugaban majalisar da sauran ’yan majalisar da kuma ita kanta Jam’iyyar APC. Sai ya gargadi shugaban majalisar, ya taka a sannu ya zama mai yi wa Jam’iyyar APC da Shugaban kasa Muhammadu Buhari biyayya, inda ya ce ba za su bari ’yan Jam’iyyar PDP su bata musu tafiya ba. Ya ce muddin Yakubu Dogara bai yi wa jam’iyyar biyayya ba, babu makawa za su tsige shi daga kan shugabancin majalisar.
Shi ma dan majalisa mai wakiltar Ringim da Taura, Malam Gausu Muhammed boyi Ringim ya ce ’yan majalisar za su ci gaba da ba Jam’iyyar APC da Shugaba Buhari goyon baya domin tabbatar da tsaro a Najeriya.
Ya ce tuni jam’iyyarsu ta yafe wa shugaban Majalisar Tarayyar laifinsa na rashin yi wa jam’iyarsu ta APC, an sami fahintar juna. Ya nuna damuwa kan matsalar rashin tsaro a kasar nan inda ya an yi shiri sosai wajen yakar mayakan kungiyar Boko Haram, kuma duk wanda gwamnati ta kama da hannu a matsalar Boko Haram ba za ta raga masa ba.
Shi kuwa dan majalisa mai wakiltar Miga da Jahun, Malam Yusif Sai’du Miga cewa ya yi rigimar majalisar ta faru ne saboda zakewar shugabanta Yakubu Dogara, inda yake neman yi mata rashin kunya. Ya ce amma yanzu sun yi nasara a kansa tunda ya rungumi gaskiya ya gane kuskurensa an gyara yanzu babu sauran matsala atsakaninsu kuma andauki duk matakan gyara domin daidaita lamuran tafiyar da majalisar.
Ya musanta jita-jitar da ake yayatawa cewa da zarar sun komo daga hutun da suke yi za su tsige shugaban majalisar, ya ce babu wannan batun tuni suka wuce wannan babi, inda ya ce maganar a tsige shugaba ba halayyar ’yan jam’iyyarsu ba ne na ’yan Jam’iyyar PDP ne.