Za mu tursasa kasar Koriya ta Arewa ta ajiye shirinta na makami mai linzami – Amurka

A daidai lokacin da ake ci gaba da cacar baki tsakanin Koriya ta Arewa da Amurka, an gano mataimakin Shugaban Amurka, Mike Pence yana ziyartar manyan sansanonin rundunar tsaron kasar guda hudu. Pence ya je Hukumar Tsaron kasar, Hukumar Binciken kasar, Sansanin Rundunae Sojin sama na Minot da Hukumar Leken asirin kasar. Sannan kuma ya […]

Za mu tursasa kasar Koriya ta Arewa ta ajiye shirinta na makami mai linzami – Amurka

A daidai lokacin da ake ci gaba da cacar baki tsakanin Koriya ta Arewa da Amurka, an gano mataimakin Shugaban Amurka, Mike Pence yana ziyartar manyan sansanonin rundunar tsaron kasar guda hudu.

Pence ya je Hukumar Tsaron kasar, Hukumar Binciken kasar, Sansanin Rundunae Sojin sama na Minot da Hukumar Leken asirin kasar. Sannan kuma ya kai ziyara sansanin sojin sama na Arewacin Dakota, inda aka ajiye makami mai linzami na Monuteman da B-52, kamar yadda Yahoo ta ruwaito.

Kafar Yahoo ta ruwaito cewa yadda Pence ke ta ziryar ziyartar wadannan sansanoni a cikin wata hudu da suka wuce, ya fi yawa a kan yadda ya ziyarci sansanonin a cikin wata bakwai da suka wuce, wanda hakan ke nuna cewa akwai lauje cikin nadi.

Duk da mataimakin shugaban ya kai ziyara, yana bayani ne a kan Koriya ta Arewa, da kuma yaki da mayakan ISIS.

Ganin cewa gwamatin Trump na fuskantar matsalolin tsaro, wannan ziyarar ba abin mamaki bane, musamman maganar matsalar shirin kera makami mai linzami da Koriya ta Arewa ke yi, yadda kasar Rasha ke ci gaba da mamaye yankin kasar Ukraine, Yakin basasar Syria, kokarin kasar China na danne Kudancin kasar da sauran rikice-rikice da kasashen da ke abota da kasar ke fama da shi.

Lokacin day a ki ziyara ofishin CIA, mataimakin shugaban ya yi godiya ga maza da matan Hukumar ta CIA bisa yadda suke aiki tukuru wajen kare mutanen kasar da kuma da kuma ‘yanci.

“A daidai wannan lokaci da kasar Koriya ta Arewa ke tayar da kura, ina tabbatar muku da cewa kasar Amurka za ci gaba da yin duk mai yiwuwa ta hanyar yin amfani da bangaren tattalin arziki, da kuma kawancen kasashe wajen tursasa kasar Koriya ta Arewa domin ta ajiye shirinta na kera makamashi mai linzami,” inji Pence, inda ya yi gargadin cewa “Za mu iya yin komai.”

Wannan ziyarar dai zai taimaka matuka wajen gyara dangantakar da ke tsakanin Shugaba Trump da Hukomomin tsaron kasar, domin a baya, shugaban ya yi maganganu marasa dadi a kan hukomomin, musamman lokacin da suka gano cewa kasar Rasha ta sa a zaben shekarar 2016 da ya yi nasara, da yadda ya kwatanta Hukumar leken asirin kasar da ‘yan Nazi na kasar Jamus, da dai sauransu.