Za mu yafe wa ’yan Boko Haram idan suka dawo da ‘yan matan Chibok lafiya – Buhari
Wakilinmu da ke Washington DC ya samu damar tattaunawa da shugaba Buhari lokacin da ya je taron Majilisar dinkin duniya a New York a kan al’amura daban-daban da suka shafi Najeriya. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya:Ranka ya dade yaya kake ganin batun cim ma muradun karni da aka shinfida, anya nahiyar Afrika za ta […]

Wakilinmu da ke Washington DC ya samu damar tattaunawa da shugaba Buhari lokacin da ya je taron Majilisar dinkin duniya a New York a kan al’amura daban-daban da suka shafi Najeriya. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya:Ranka ya dade yaya kake ganin batun cim ma muradun karni da aka shinfida, anya nahiyar Afrika za ta iya cim ma lokacin da aka shata?
Buhari: kasashen Afrika kowa ya ji a jikinsa, babu abin da mu Afrika muke so illa zaman lafiya da wadata, domin ta kowace irin gwamnati ce kuma ta kowace irin jam’iyya ce, fatanta shi ne ta tabbatar da kasarta ta zauna lafiya, an samar wa al’umma aikin yi, kuma ya zamanto suna iya noma abincin da za su ci har ma su sai da wa wadansu kasashe daban. Kuma ta fuskar tsaro suna zaune lafiya, kana akwai wutar lantarki, akwai hanyoyi masu kyau, akwai ruwan sha, akwai makarantu, akwai asibiti.Wannan shi ne burin kowace irin gwamnati, balle ma na kasashenmu masu tasowa.
Aminiya:A da ana da muradu 8, yanzu an mayar da su 12, yaya kake kallon wannan lamari, ba za a bar nahiyar Afirka a baya ba?
Buhari:To kasashen Afirka an riga an tsere musu, duk wanda ya fi ilmin zamani, musammam abin da ya shafi kimiyya, ya zo ya yi ma’aikatu da yawa, ya sama wa mutanensa aiki, ya tabbatar yana noma abin da zai ci ba tare da sai ya saye ba, ya tabbatar cewa jami’an tsaronsa an horar da su suna son kasarsu, suna aiki ba da son rai ba, an yi musu bariki, yaransu suna zuwa makaranta ba tare da damuwa ba,idan ba su da lafiya suna zuwa asibiti, albashi yana zuwa a kan kari yadda ya kamata, shi ne zama lafiya da ci gaba.
Aminiya:A cikin jawabinka a Majilisar dinkin duniya ka ce Najeriya ta mayar da hankali wajen yaki Boko Haram, amma sai ga shi an yi taro game da tsaro wanda ya shafi Najeriya ba ka wurin kuma ba wakilinka, me ya faru?
Buhari:To mutum ba sai ya sani ba zai je, ko ka je abin da ba ka da masaniya ne a kai?
Aminiya:Wato ba a sanar daku ba?
Buhari:Ba a sanar da mu ba, yaya za ayi mu sani kuma mu ki zuwa? yanzu cikin mako guda, cikin satin da aka rantsar da ni na je Nijar da Chad, ba ya da kirana da aka yi a Jamus da kuma manyan kasashen duniya masu arziki su 7, kuma naje kamaru, amma sai da na dawo taro da kasashen nan 7 na tafi Kamaru, haka kuma na je jamhuriyar Benin, kuma har wayau mun shirya taro na shugabbanin sojoji na wadannan kasashen,wato Benin da Chadi da Kamaru Nijar da Najeriya, muka hadu a Abuja. Bayan wannan taron sai kuma ministocin tsaro suka hadu, kana mu shugabannin kasashen muka hadu. To me za mu yi fiye da wannan? sai dai kawai mu zo domin mu cim ma matsaya a kan yadda za mu tafiyar da yankin Chadi ga kasashen da ke kewaye da tafkin na Chadi.
Aminiya:Wani lokaci can baya ka ce ba za a wuce watan Satumba ba za ka fitar da sunayen ministocinka, amma ga shi sai da aka kai daf da karshen watan sannan ka aika sunayen, me ya faru?
Buhari:To kar ka manta cewa ‘yan majilisa sun yi, hutu idan muka aika wane ne za mu aika mawa? Da suka dawo ba ka ga mun aika ba, yanzu muna jira ne mu ji wadanda ba su yarda da su ba da kuma dalilin da ya sa ba su yarda da su ba sai a cire su.
Aminiya: A cikin jawabin da ka yi ka zargi wadansu kasashe da kawo wa Najeriya tarnaki a yakin da take yi da cin hanci da rasahawa, ko za ka kara haske kan abin da kake nufi?
Buhari:Sani kowa ne jiragen ruwan da suke zuwa su dauki mai a Najeriya su kai shi inda za a sai da duk jiragen na kasashen waje ne kuma akwai doka na jiragen ruwa cewa duk kayan da suka dauka za a rubuta inda suka dauki kayan da kuma inda zasu kai su. Sai ya zamana ciki binciken da muka fara yin a satan man Najeriya akwai jiragen ruwan da suke daukar mai amma ba za su tafi inda aka yi za su kai man ba, sai a cikin teku za a juye wa wani jirgi daga nan shi kuma sai ya yi gaba da man. Kuma idan aka je aka sayar sai a bude ajiyar banki a waccan kasar da jirgin da aka juye mawa ya kai, alhali daga Najeriya ba kasar da aka yi za a kai man ke nan ba, kuma ba a ciki ajiyan Najeriya za a sanya kudin ba, kodayake ba kasar da suka ce ke nan za su kai man ba, sai dai a ajiye kudin a cikin ajiyar bankin wadansu mutane, kuma sau tari wadansu kasashen suna sane. Shi ya sa na ce abin da na ce.
Aminiya: Ina maganar ‘yan matan Chibok ya kwana ne, domin wasunsu da suka samu tserewa suna nan Amurka?
Buhari: To wadannan da suka zo nan Amurka ni ban san wanda ya kawo su ba, amma tun da ‘yan Najeriya ne, domin ko sun yi amfani da takardar iznin shiga wata kasa ta Najeriya, wato Fasfo, to har yanzu ‘yan Najeriya ne.Yanzu kikarin da wannan gwamnati take yi shi ne ta san sauran ‘yan matan nan a ina suke? Wane hali suke ciki?saboda wannan yana sawa yadda sojoji suke nema su yi da su ‘yan Boko Haram muna damuwa kwarai da gaske kada su kai yadda idan aka fada wa ‘yan Boko Haram su cutar da su, shi ya sa ake magana da shugabannin ‘yan Boko Haram wadanda aka sani, cewa idan za su ba mu ‘yan matan nan gaba daya kamar yadda suka dauke su kuma cikin lafiyarsu, to mu za mu yafe musu laifin da suka yi wa Najeriya, duk da dai sun kashe ‘yan Najeriya da yawa.
Aminiya: Me gwamnatin za ta yi domin rage zaman banza da shaye-shaye a tsakanin matasa?
Buhari:To na farko dai maganin shaye-shaye shi ya sa ake da ‘yan sanda da kuma hukumar yaki da shan miyagun kwayoyi (NDLEA) inda ake da kwararru, idan magungunan mara sa tasiri ne ko masu cutarwa ne muna magana da su manyan kasashen da ake kawo wadannan muggan kwayoyin cewa duk wanda aka samu da wannan laifin babu afuwa za a hukunta shi daidai da yadda doka ta tanada, kuma muna fata iyaye suna samun lokaci suna sa wa ‘ya’yansu ido, ba zuwa makaranta ba su dawo a ba su abinci ba, a’a kamata ya yi iyaye su gane shin wadanne irin abokai ne ‘ya’yansu suke da su? kuma su taimaka wa gwamnati, su ba ta bayanin inda suka san ana sayar da wadannan kwayoyin masu yi wa mutane illa, ko kuma su sanar da jami’an hukumomin nan masu wannan aiki don a kama su, a san daga ina suke kawo wadannan kwayoyin.To yanzu matsalar ta kai ga cewa har su masu shan kwayoyin sune ke yin kwayoyin da kansu ko kuma su rika shan magungunan tari wanda ya wuce ka’ida domi kawai su yi maye, wannan abu ne mai wahala, amma ya kamata iyaye su ma su shigo cikin wannan lamari ba wai gwamnati za a bari da kashin mahaukacin kare ba.