Za mu yaki bidi’o’in aure da mutuwa a yankin Yamma -Sheikh Mas’ud Ibrahim
A karashen makon da ya gabata ne kungiyar Izalatul Bidi’a Wa Ikamatus Sunna, karkashin shugabancin Shaik Bala Lau ta gudanar da babban taro a Legas, inda kabilu daga jihohin Najeriya da kasashen Afirka ta Yamma suka hadu. Taken taron shi ne, Hadin Kai da Zaman Lafiya don ci gaba mai dorewa. Aminiya ta samu tattaunawa […]

A karashen makon da ya gabata ne kungiyar Izalatul Bidi’a Wa Ikamatus Sunna, karkashin shugabancin Shaik Bala Lau ta gudanar da babban taro a Legas, inda kabilu daga jihohin Najeriya da kasashen Afirka ta Yamma suka hadu. Taken taron shi ne, Hadin Kai da Zaman Lafiya don ci gaba mai dorewa. Aminiya ta samu tattaunawa da Sheikh Mas’ud Ibrahim daya daga cikin fitattun Malaman kabilar Yarabawa kuma mataimakin shugaban Majalisar malami na jihohin Yamma, inda ya bayyana hadin kan da aka samu a tsakanin kabilun Yarabawa da Hausawa da kuma bidi’o’in da suke so su yaka a tsakanin kabilun Yarabawa. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Me kake ganin ya kawo hadin kai a tsakanin kabilar Yarabawa da Hausawa a tafiyar kungiyar Izala?
Sheikh Mas’ud: Tun shekarun 1960 aka samu malamai daga kabilar Yarabawa da suke yin kira da a tsayar da sunnah a daina bidi’a. A rika tsayar da gemu da nada rawani da tsare mata da sanya kayan Musulunci. Daga bisani sai aka samu haduwa tsakanin Yarabawa da Hausawa kan wannan akida aka tafi tare.
Aminiya: Wane hadin kai da dankon zumunci kake ganin taron zai samar a tsakanin Hausawa da Yarabawa?
Sheikh Mas’ud: Muna da tabbacin cewa taron zai kara wa Musulunci daukaka tare da kara hada kan Yarabawa da Hausawa, musamman ma saboda kawo wa’azin a tsakiyar Yarabawa, kodayake ba a samu an yi wa’azin da Yarabanci da yawa ta yadda Yarabawan za su amfana sosai ba, amma duk da haka da babu gara kadan din. Saboda haka kawo wa’azin a nan Legas zai sa a samu karin dankon zumunci.
Aminiya: A matsayinku na Yarabawa wadanne bidi’o’i ne suke ci muku tuwo a kwarya da kuke so a kawar da su?
Sheikh Mas’ud: Gaskiya daga cikin manya-manyan bidi’o’in da suke walahar da mu su ne, na farko batun aure, inda za ka ga mutane suna yin lalata da mata, wani lokaci har ta kai ga sun yi musu ciki kafin su aure su.Wadansu na ganin tunda har yaron da yarinyar sun yarda da junansu suna ganin babu komai, amma mu muna nuna musu cewa ba haka Musulunci ya nuna ba. Wannan bidi’a tana damunmu kwarai da gaske. Shi ya sa muka tashi tsaye muna fadakar da mutane illar wannan abu. Sai batun taron makoki na kwanaki bakwai ko arba’in ko shekara. A wadansu wurare sai ka dauka biki ake yi. Shi ma abu ne da yake damunmu. To amma akwai wadansu malamai da ke daure wa abin gindi, saboda ta nan suke samun abinci. Su ma malaman muna fadakar da su, muna nuna musu illar haka.
Aminiya: Wane mataki kuke dauka kan batun fadan kabilanci da ke aukuwa tsakanin Hausawa da Yarabawa inda za ka ga ana kashe juna?
Sheikh Mas’ud: Babu abin da zai yi maganin wannan matsala sai karantarwa da wa’azi. Idan mutane ba su fahimci addini sosai ba, yana da wuya su bar kabilanci. Babbar hanyar maganin wannan ita ce malamai su karantar da al’umma su gane hadarin da ke cikin kabilanci. Muna gode wa Allah, muna fadakar da mutane su gane illar fadan kabilanci. Idan aka ci gaba da fadakar da mutane ta kowane bangare babu shakka za a samu nasara.