Za mu yaqi masu ci da gumin ‘yan fim – Afakallah

Isma’ila Na’abba Afakallah shi ne sabon Shugaban Hukumar Tace Fina-Finai da dab’i ta Jihar Kano, furodusa ne a masana’antar fina-finan Hausa. Wannan ne lokaci na farko da aka fara dauko dan fim aka ba shi shugabancin wannan hukuma. A tatatunawarsa da Aminiya ya bayyana irin abubuwan da hukumar za ta yi ga ’yan fim da […]

Za mu yaqi masu ci da gumin ‘yan fim – Afakallah
Za mu yaqi masu ci da gumin ‘yan fim – Afakallah

Isma’ila Na’abba Afakallah shi ne sabon Shugaban Hukumar Tace Fina-Finai da dab’i ta Jihar Kano, furodusa ne a masana’antar fina-finan Hausa. Wannan ne lokaci na farko da aka fara dauko dan fim aka ba shi shugabancin wannan hukuma. A tatatunawarsa da Aminiya ya bayyana irin abubuwan da hukumar za ta yi ga ’yan fim da kuma harkar:

Aminiya: Wadanne sababbin tsare-tsare wannan hukuma za ta yi ga masana’antar fim a karkashin shugabancinka?
Afakallah: Babu shakka akwai kalubale mai yawa, sai dai da taimakon Allah da dacewa da sanin makamar abubuwa insha Allah za a yi nasara. Kasancewata daya daga cikin ’ya’yan wannan masana’anta za mu yi kokari wajen ganin an dawo da martabar fim, mu bunkasa harkar. Za mu yi kokarin farfado da gidajen kallo ma’ana silima ta yadda za su taimaka wajen ganin ’yan fim da suke sa kudinsu a harkar sun mayar da kudinsu. Kuma za mu sa a yi fina-finai masu inganci tare da kula da addini da al’adunmu, kuma mu yi kokarin inganta kasuwar fim da habakata yadda za ta yi gogayya da takwarorinta na duniya. Sannan zan kafa kwamiti mai suna Kannywood Debelopment Committee da zai yi duba yadda harkar za ta bunkasa, saboda akwai abubuwan ci gaba a yanzu da ba mu so a ce an bar fim din Hausa a baya. Ya zama cewa ko allura ce ta fadi kasa, karar faduwarta ya fito ya yi daidai da yadda mai kallo zai gamsu da haka.  Haka za mu hada kai da Masarautar Kano don a fito da abubuwan al’adunmu masu kyau da kuma ainihin gargajiyarmu. Kuma za mu fito da irin sadaukarwar sarakunanmu na baya a cikin fina-finanmu, idan muna son yin fim game da abin da ya faru shekara 50 baya, to dole sai mun hada kai da masarauta don fito da ainihin abin da ake nema. Shi fa fim ba don a ci abinci kawai ake yin sa ba, ana yi ne don a yi kudi. Idan mutum ya yi fim sai ya yi shekara 30 yana cin moriyarsa. Idan kika duki fim din Mother India har yanzu ana sayar da shi. Haka Sangaya a Kannywood har yanzu ana cinkinsa.  
Kasancewar alhakin wannan hukuma ne kula da dab’i, za mu sa ido a kan irin rubuce-rubucen da ake fitarwa, don ganin sun yi daidai da al’adu da addininmu ta yadda za mu tace mu rairaye duk kalaman batsa. Haka su ma gidajen kallo da wuraren gudanar da bukukuwa za mu yi kokarin ganin an tafiyar da su bisa doka da oda, ba tare da wani abu na keta alfarmar addini ko al’ada ba.  
Aminiya: Masu harkar fim na kuka da yadda ake yi musu satar fasaha, ta yaya hukumar za ta taimaka a rage wannan matsala?
Afakallah: Matsalar satar fasha aba ce da ake fama da ita a duniya, duk da yake a kasahsen da suka ci gaba ana samun raguwar lamarin. Babu wata tsayayyar doka da ta hana satar fasaha, kuma hukumar da ke kula da lamarin ba ta da kayan aikin da za ta gudanar da aikinta. A duk lokacin da wani furodusa yake son su yi masa aiki to fa shi zai dauki nauyin komai tun daga motar hawa da kudin daukar ’yan sanda da sauransu. Ina son yin amafani da wannan dama in yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa ido a kan wannan hukuma a wadata ta da kayan aiki tare da neman shawarwari daga masu ruwa da tsaki a harkar. Satar fasahar nan ana yin ta ne tun daga can kasa, ma’ana daga wurin da ake buga fim. Idan an kama mutum a kai shi kotu don ya fuskanci hukunci. Mu kuma a namu bangaren za mu yi kokarin ganin mun yaki masu kwafa a intanet (downloading). Ba zai yiwu mutum ya sa jarinsa ya kashe kudinsa ya yi fim sannan wani ya je ya rika tura fim din a waya yana sayarwa Naira 20 ko 50 ba. Za mu yaki masu ci da gumin ’yan fim ta kowace hanya. Ba za mu yarda da ’yan downloading ba, domin ba zai bunkasa harkar ba, mu kuwa muna neman duk wata hanya da za ta habaka wannan sana’a don ganin masu sana’ar sun ci moriyarta yadda ya kamata.
Aminiya: Dokokin hukumar an tsara su ne a shekara 2002, masana na ganin akwai bukatar a yi gyara ga wasu dokokin lura da canzawar abubuwa, me za ka iya yi a kan haka?
Afakallah: Wannan na daga cikin abubuwan da zan yi kokarin tabbatuwarsu. Za mu yi kokari da masu ruwa da tsaki a harkar don fitar da dokoki a hukumar. Za mu sake duba dokokin mu ga wadanda za a yi wa gyara za mu cire wadanda muke ganin akwai bukatar yin hakan. Amma hakan ba zai samu ba, dole sai mun yi duba yanayi da yadda abubuwa za su dace da zamani.
Aminiya: Akwai makudan kudin tallafi da aka ce Gwamnatin Tarayya da hadin kan Bankin Duniya sun fitar don masu fim a kasar nan, da ’yan fim din Kudu suka fi amfana, wane kokari za ka yi wajen ganin Kannywood sun amfana daga tallafin?
Afakallah: Wannan ma na cikin abubuwan da za mu yi kokari kansu, saboda abin na damunmu. Idan aka ce a Arewa ba mu amfana ba, ba a yi karya ba, domin mutum bakwai ne kacal suka samu wannan tallafi kuma babu wanda aka ba Naira miliyan 10, sai mutum 19 da aka kai Indiya. Amma a Kudu mutane da dma sun amfana da kudin, haka kuma an kai mutane sama da 50 kasar Amurka. Akwai kuma wani sashi da za a yi na fitar da kayan yadda aka ce mutane 80 ne za su amfana, a ciki kuma mutum biyu ne daga Arewa. Hakan ya sa muka rubuta takarda wadda ta janyo aka dakatar da abin gaba daya tare da bincikar abubuwan da aka yi a baya. Za mu yi kokari a matakin jiha wajen ganin mun farauto rabonmu daga wannan tallafi insha Allah.
Aminiya: A lokutan baya an samu baraka tsakanin ’yan fim da kungiyar ’yan fim din da hukumarka, wane yunkuri za ku yi don dinke barakar baya? Afakallah: Abin da yake faruwa shi ne akwai bukatar a samu hadin kai a kungiya. Ni dan kungiya ne na san muhimmancinta. Lallai za mu karfafa kungiya, don mafi yawan lokuta gwamnati ta fi taimaka wa jama’a a kungiyance. Abubuwan da aka samu na sabani a baya, insha Allah za mu tabbatar ba su sake faruwa ba.